Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

5 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Lallai ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai haƙiƙa Shaiɗan ya shiga tsakanina da sallata da kuma karatuna, yana rikitar da ni, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku", sai ya ce: Sai na aikata hakan sai Allah Ya tafiyar da shi daga gareni.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiya ne abin gasgatawa: "Lallai cewa halittar dayanku ana tarota a cikin mahaifiyarsa yini arba'in da dare arba'in. Sannan ya zama gudan jini tamkarsa, sannan ya zama gudan tsoka tamkarsa, sannan a aiko masa da Mala'ika, a yi masa izini da kalmomi hudu, sai ya rubuta arzikinsa da ajalinsa da aikinsa, dan wuta ne ko dan Aljanna ne, sannan ya busa rai a cikinsa. Lallai dayanku zai yi aiki da aikin 'yan Aljanna har ya zama tsakaninsa da ita bai zamo ba sai zira'i, sai littafi ya rigaya agare shi sai ya yi aiki da aikin 'yan wuta sai yashiga wutar. Kuma cewa dayanku zai yi aiki da aikin 'yan wuta har ya kasance tsakaninsa da ita bai zamo ba sai zira'i, sai littafi ya rigaya akansa, sai ya aikata aikin 'yan aljanna sai ya shigeta".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«‌Yayin da (Mala’ika) Jibrilu yake zaune a wurin Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wata ƙara daga samansa, sai ya ɗaga kansa sama, sai ya ce: Wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, ba'a taɓa buɗe ta ba sai yau, sai wani Mala'ika ya sauko daga cikinta, sai ya ce: Wannan wani Mala'ika ne da ya sauko ƙasa, kuma bai taɓa sakkowa ba sai yau, sai ya yi sallama, ya ce: Ka yi albishir da haske biyu da aka ba ka su, wanda ba'a bawa wani Annabi kafinka ba; Ita ce Fatihatul Kitab, da ƙarshen suratul Baƙarah, ba za ka karanta wani harafi daga cikinsu ba sai an ba ka shi».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«‌Addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa a ɓoye abar karɓa ce, a daidai kansa akwai wani Mala'ika wanda aka wakilta a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce: Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin haka».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Mala'iku ba sa tafiya da ayarin da a cikinsa akwai kare ko ƙararrawa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi