Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

34 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin tafiya, sai ya tafi wata buƙatarsa, sai muka ga wata tsuntsuwa tare da 'yayanta biyu, sai muka ɗauke su, sai tsuntsuwar ta zo tana fakan-fakan (tana nemansu), sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: «‌Waye ya raba wannan da ɗanta? ku maida mata da ɗanta», kuma sai ya ga wasu ramin tururuwa wanda muka ƙona shi, sai ya ce: «‌Waye ya ƙona wannan?» mukace: Mune. Ya ce: «‌Babu wanda yake yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta».
Ingantacce ne Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Lallai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka, sai ya ce: "Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su, sabo da haka mutane sun kasu biyu: Mai biyayya ga Allah kuma mai tsoronSa mai girma a wajen Allah, da kuma fajiri taɓaɓɓe wulaƙantacce a wajen Allah, mutane 'ya'yan (Annabi) Adam ne, kuma Allah Ya halicci Annabi Adam daga turɓaya, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ya ku mutane lallai Mun halicce ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wurin Allah shi ne mafificinku a tsoron Allah, lallai Allah Masani ne kuma mai ba da labari [Al-Hujrat: 13].
Ingantacce ne Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki wata ƙaramar runduna sai ya shugabantar da wani mutum daga cikin mutanen Madina, kuma ya umarcesu da su yi masa biyayya, sai (mutumin) ya yi fushi, sai ya ce: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai umarce ku ku bini ba? suka ce: Ya umarcemu. (Sai) Ya ce: Ku haɗa mini itatuwa, sai suka haɗa masa, sai ya ce: Ku kunna wuta, sai suka kunnata, sai ya ce: Ku shigeta, sai suka yi niyyar (shiga), sai wasu daga cikinsu suka riƙe wasu, suna cewa: Mun gujewa wuta ne zuwa wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, basu gushe ba har sai da wutar ta mutu, sai fushinsa ya gushe, sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: «Da a ce sun shigeta da ba zasu fita daga cikinta ba har zuwa ranar alƙiyama; biyayya tana kasancewa ne kawai a aikin alheri».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Kwatankwacin tsayayye ga iyakokin Allah da mai afkawa cikinsu, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka yi kuri'a a jirgin ruwa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa, wadanda ke kasansa sun kasance idan sun nemi ashayar da su ruwa sai sun wuce wadanda ke samansu, sai suka ce: Dama a ce zamu tsaga wata kafa a rabonmu ba mu cutar da wandanda ke samanmu ba, idan sun barsu da abinda suka yi nufi za su halaka gaba dayansu, idan suka yi riko da hannayensu za su tsira, sai su tsira gaba dayansu".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Ku isar game da ni koda aya daya ce, kuma ku zantar game da Banu Isra'ial babu laifi, duk wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi mazauninsa a wuta".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Za'a samu babakere da wasu al'amuran da zaku kisu" suka ce : Ya Manzon Allah mezaka umarcemu? Ya ce: "Ku bada hakkin da ya wajaba akanku, kuma ku roki Allah hakkinku ".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su: Waye Muhammad a cikinku? alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide a tsakaninsu, sai muka ce : Wannan farin mutumin wanda ke kishingide. Sai mutumin ya ce da shi: Ya kai Dan Abdul Mudallib sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: "Hakika na amsa maka". Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji haushi na a ranka? sai ya ce: "Ka tambayi abinda ya bayyana gareka" sai ya ce: Ina tambayarka dan Ubangijinka da Ubangijin wadanda suka gabaceka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane gaba dayansu? sai ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu yi salloli biayr a yini da dare? ya ce: "Eh ya Allah ne.” ya ce Ina maka magiya da Allah shin Allah ne Ya umarceka da mu yi azumin wannan watan a shekara? ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce; Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawan mu? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Eh ya Allah". sai mutumin ya ce; na yi imani da abinda ka zo da shi, kuma ni manzo ne na wadanda ke bayana cikin mutane na, Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna zalinci, wanda ya gasgata su akan ƙaryarsu kuma ya taimakesu akan zalincinsu to ba ya ta tare da ni, nima bana tare da shi, kuma ba zai gangarowa Alkausara ba, wanda bai gasgatasu akan ƙaryarsu ba kuma bai taimakesu akan zalincinsu ba to shi yana tare da ni, nima ina tare da shi, kuma zai zo Alkausara".
Ingantacce ne Ahmad ne ya rawaito shi