Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

72 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lokacin da ya fita zuwa Hunain ya wuce wata bishiya ta mushrikai ana ce mata: Ma'abociyar rataya, suna rataye makamansu akanta, sai suka ce: Ya Manzon Allah, ka sanya mana ma'abociyar rataya kamar yadda suke da ma'abociyar rataya, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki ya tabbata ga Allah! wannan kamar yadda mutanen Musa sukace ne: {Ka sanya mana wani ubangiji kamar yadda suke da iyayen giji} [Al-Aaraf: 138] Na rantse da wanda raina yake a hannunsa zaku bi hanyar wadanda ke gabaninku".
Ingantacce ne Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
"Kada ku ce : Allah Ya so wane ma ya so, saidai ku ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so".
Ingantacce ne a baki dayan hanyoyin sa Abu Dawud da Nasa'i cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi
«Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Mabuɗan gaibu biyar ne, {Lalle, Allah a wurinSa kawai sanin yaushe Alkiyama zata tashi yake, kuma Yanã saukar da ruwan sama, kuma Yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai kuma wani rai bai san abin da yake aikatãwa a gõbe ba, kuma wani rai bai san a wace ƙasã yake mutuwa ba. Lalle Allah Masani ne Mai ƙididdidigẽwa}».
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Lallai Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Zai cewa 'yan aljanna: Yaku 'yan aljanna? sai su ce: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, sai Ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Dan me ba zamu yarda ba alhali Ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarKa ba? Sai Ya ce: Ni zan baku mafifici daga hakan, sai su ce: Ya Ubangiji, wane abu ne maffifici daga hakan? Sai Ya ce: Zan saukar muku da yardata, ba zan yi fushi daku ba a bayansa har abada".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Duk wanda ya gamu da Allah ba ya hada wani abu da shi to kuskurensa ba zai cutur da shi tare da shi ba, wanda kuwa ya mutu alhali yana yin shirka da shi wani kyakkyawan aikinsa ba zai amfane shi tare da shi da komai ba"
Ingantacce ne Ahmad ne ya rawaito shi
«Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallatai» ta ce; Da badan haka ba da an bayyanar da ƙabarinsa, sai dai cewa an ji tsoron a riƙe shi a matsayin masallaci.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Ku kusanto ku daidaita, ku sani cewa babu wani daga cikinku da zai tsira da aikinsa". Suka ce: Ya Manzon Allah koda kaine?ya ce: "Koda nine sai dai idan Allah Ya lulluɓeni da rahamarSa da kuma falalarSa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi