Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

55 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi girma a wurin Allah? ya ce: " Ka sanyawa Allah kishiya alhali Shi Ya halicceka" Na ce: Lallai wannan mai girmane, na ce: Sannan wanne? Ya ce: "Ka kashe danka; dan tsoron ya ci tare da kai". Na ce: Sannan wanne? ya ce: "Ka yi zina da matar makocinka".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai kare ko hoto a cikinsa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Lallai Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Zai cewa 'yan aljanna: Yaku 'yan aljanna? sai su ce: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, sai Ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Dan me ba zamu yarda ba alhali Ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarKa ba? Sai Ya ce: Ni zan baku mafifici daga hakan, sai su ce: Ya Ubangiji, wane abu ne maffifici daga hakan? Sai Ya ce: Zan saukar muku da yardata, ba zan yi fushi daku ba a bayansa har abada".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallatai» ta ce; Da badan haka ba da an bayyanar da ƙabarinsa, sai dai cewa an ji tsoron a riƙe shi a matsayin masallaci.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Ku kusanto ku daidaita, ku sani cewa babu wani daga cikinku da zai tsira da aikinsa". Suka ce: Ya Manzon Allah koda kaine?ya ce: "Koda nine sai dai idan Allah Ya lulluɓeni da rahamarSa da kuma falalarSa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi