Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

123 daga cikin katuna 839

Cire tacewa

Mai ruwaya

Nuna duk masu ruwaya (54)
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Mu’azu yana bayan shi a kan jaki, Ya ce: Ya Mu’azu Ɗan Jabal!!)). Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa, Ya ce; Ya "Mu’azu" Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa sau uku [ya faɗa], ya ce: Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne da gaske daga zuciayarsa sai wuta ta haramta a gareshi)). Ya ce: Ya Ma’aikin Allah shin ba na ba mutane labarin nan ba domin su yi murna? Ya ce: Za su saki jiki. Sai Mu’azu ya ba da labarin bayan rasuwar Ma’aikin Allah gudun kada ya ɓoye ilimi.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ga mai tabo mai tabon Abdulƙais: «‌Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Allah ba Ya duba zuwa wanda ya ja tufansa (ƙasa) dan girman kai".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: Tafiya ta yanke min, ka ba ni dabbar da za ta ɗaukeni, sai ya ce: "Ba ni da ita", sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan shiryar da shi ga wanda zai ba shi dabbar da za ta ɗaukeshi, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatashi".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin" Aka ce: Wa ya Manzon Allah? Ya ce: "Wanda ya riski iyayen sa lokacin girma, ɗayan su ko su biyun amma bai shiga Aljanna ba".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi