Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

123 daga cikin katuna 839

Cire tacewa

Mai ruwaya

Nuna duk masu ruwaya (54)
"Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Da a ce mutane suna sanin abinda ke cikin kiran sallah (na lada) da kuma sahu na farko sannan ba za su samu ba sai idan sun yi ƙuri'a a kansa da sun yi ƙuri'a, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin gaggawa (zuwa sallah a farkon lokaci) da sun yi gasar zuwa gare shi, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin sallar dare (Issha) da Asuba da sun zo musu koda da jan ciki ne».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga aikin alheri da kuma zunubi, sai ya ce: "Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma kaƙi mutane su yi tsinkaye akansa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Kowa ne aikin alheri sadaka ne".
Ingantacce ne Bukhari ne ya ruwaito shi daga hadisin Jabir, kuma Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Huzaifa.
"Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi ".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yake, a tsakaninsu akwai wasu al'amura masu rikitarwa da yawa daga mutane ba sa saninsu, wanda ya kiyaye shubuhohi ya kuɓuta a addininsa da mutuncinsa, wanda ya afka cikin shubuhohi ya afka a cikin haram, kamar mai kiwo ne da yake kiwo a gefen shinge ya kusata ya yi kiwo a cikinsa, ku saurara! lallai kowane sarki yana da shinge, ku saurara! lallai shingen Allah shi ne abubuwan da ya haramta, ku saurara lallai! Lallai a jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru jiki ya gyaru dukkaninsa, idan ta ɓaci jiki ya ɓaci dukkaninsa, ku saurara! ita ce zuciya".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafifici a wurin Allah? ya ce: "Sallah akan lokacinta", Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: "Sannan biyayya ga mahaifa" Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: Yaki a tafarkin Allah" ya zantar dani su, da na nemi ya kara min da ya karamin.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai ɗayanku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: Ina shaida wa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce; Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sannan ya ce; Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa sallah, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa tsira, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sai ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah daga zuciyarsa zai shiga aljanna".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi