Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

1 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Cewa wani mutum ya shiga masallaci a ranar Juma'a ta wata ƙofar da ta kasance daura da gidan hukunci, alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana tsaye yana huɗuba, sai ya fuskanci Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tsaye, sannan ya ce: Ya Manzon Allah, dukiyoyi sun halaka hanyoyi sun yanke, ka roƙa mana Allah Ya shayar da mu, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ɗaga hannayensa, sannan ya ce: «Ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah Ka shayar da mu» Anas ya ce: Na rantse da Allah bama ganin wani girgije ko wani yanki na girgije kuma tsakaninmu da Sal'a babu wani ɗaki ko gida, ya ce: Sai wani girgije ya ɓullo ta bayanmu kwatankwacin garkuwa, lokacin da ya tsaya a tsakiyar sama sai ya yaɗu, sannan ya zubar da ruwa, na rantse da Allah, bamu ga rana ba tsawon kwana shida, sannan wani mutum ya shigo daga waccan ƙofar a wata Juma'ar, alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana tsaye yana huɗuba, sai ya fuskance shi a tsaye, sai ya ce: Ya Manzon Allah, dukiyoyi sun halaka, hanyoyi sun yanke, ka roƙa mana Allah Ya ɗauke mana ruwan, ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ɗaga hannayensa, sannan ya ce: «Ya Allah Ka saukar da ruwan a gefenmu ba akanmu ba, ya Allah akan tuddai da duwatsu, da cikin kwarrai, da matsirar bishiyoyi» ya ce: Sai ya ɗauke, sai muka fita muna tafiya cikin rana, Sharik ya ce: Na tambayi Anas ɗan Malik: Shin shine mutumin nan na farko? sai ya ce: «Bansani ba».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi