Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

5 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Manzon Allah - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya yi kabbara a sallah, sai ya yi shiru ɗan wani lokaci gabanin fara karatu, sai na ce: Ya manzon Allah, fansarka baba na da Baba ta, kana ganin shirun da kake yi tsakanin kabbara da karatu, me kake cewa? ya ce: Ina cewa: Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwan ƙanƙara kuma mai tsananin sanyi".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayin wata sallah ba bayan saukar: {Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} [al-Nasr: 1] ta sauka gare shi sai ya ce a cikinta (sallar): "Tsarki ya tabbatar maKa Ubangijinmu da godiyarKa ya Allah Ka gafarta mini'.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla: "babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne godiya tasa ce, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, ba mai bayar da abin da Ka hana, mai wadata wadatarsa bata amfanar da shi (komai) a wajenKa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yin addu'a yana cewa: "Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)". A cikin wani lafazin na Muslim: "Idan dayanku ya gama tahiyar karshe, to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa hudu: Daga azabar kabari, da fitinar rayuwa da mutuwa, da sharrin Mai yawan yawo makaryaci (Jujal).
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi