Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

4 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Lallai ya kasance yana yin kabbara a kowacce sallar farilla da watanta, a Ramadan da waninsa, sai ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa, sannan ya yi kabbara a yayin da yake yin ruku'u, sannan ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan ya ce: Ya Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa kafin ya yi sujjada, sannan ya ce: Allah ne mafi girma a yayin da yake tafiya ƙasa don yin sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa daga zama a raka'a ta biyu, zai aikata haka a kowacce raka'a, har sai ya gama sallar, sannan ya ce a yayin da yake juyawa: na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sallar manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce sallarsa har ya bar duniya.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Cewa Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo, sai ya yi sallah, sannan (ya zo) ya yi sallama ga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi-sai ya amsa masa kuma ya ce: Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba", sai ya koma ya yi sallah kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo ya yi sallama ga-Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Koma ka yi sallah, domin cewa kai baka yi sallah ba" sau uku, sai ya ce: Na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan iya yin wacce ta fita ba, to ka koya mini, sai ya ce: "Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbara, sannan ka karanta abinda ya sawwaka tare da kai na Alkur'ani, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, sannan ka dago har sai ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, sannan ka dago har sai ka natsu a zaune, kuma ka aikata hakan acikin sallarka gaba dayanta".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta {قل يأيها الكافرون} da {قل هو الله أحد} a raka'o'i biyu (kafin sallar) Asuba.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta".
Ingantacce ne Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi