Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

6 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Lallai ya kasance yana yin kabbara a kowacce sallar farilla da watanta, a Ramadan da waninsa, sai ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa, sannan ya yi kabbara a yayin da yake yin ruku'u, sannan ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan ya ce: Ya Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa kafin ya yi sujjada, sannan ya ce: Allah ne mafi girma a yayin da yake tafiya ƙasa don yin sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa daga zama a raka'a ta biyu, zai aikata haka a kowacce raka'a, har sai ya gama sallar, sannan ya ce a yayin da yake juyawa: na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sallar manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce sallarsa har ya bar duniya.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah, haka nan in zai yi kabbara dan ruku'u, haka idan kuma zai ɗago kansa daga ruku'u sai ya ɗagasu, kuma ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gare ka, ya kasance ba ya yin haka a cikin sujjada.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani : "(Tsarkakan) Gaisuwa ta tabbata ga Allah, da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne". Acikin wani lafazi na su: "Lallai cewa Allah Shi ne aminci, idan dayanku ya zauna a cikin sallah to ya ce: (Tarakakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agreka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah daalbarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari. Idan ya fadeta za ta samu kowanne bawan Allah nagari a sama da kasa, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonsa ne, sannan ya zabi abin yake so ya roka".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Cewa Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo, sai ya yi sallah, sannan (ya zo) ya yi sallama ga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi-sai ya amsa masa kuma ya ce: Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba", sai ya koma ya yi sallah kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo ya yi sallama ga-Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Koma ka yi sallah, domin cewa kai baka yi sallah ba" sau uku, sai ya ce: Na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan iya yin wacce ta fita ba, to ka koya mini, sai ya ce: "Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbara, sannan ka karanta abinda ya sawwaka tare da kai na Alkur'ani, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, sannan ka dago har sai ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, sannan ka dago har sai ka natsu a zaune, kuma ka aikata hakan acikin sallarka gaba dayanta".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai: Akan goshi sai ya yi nuni da hannunsa akan hancinsa, da hannaye, da gwiwoyi, da gefunan diga-digai, kuma kada ka tufke tufafi ko gashi".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Lallai wasu mutane sun zo wa Sahlu ɗan Sa'ad Al-sa'idiy alhali sun yi musu a sha'anin minbarin (Manzon Allah) katakwayensa na mene ne, sai suka tambaye shi game da hakan, sai ya ce: Na rantse da Allah ni na san na mene ne su, haƙiƙa na gan shi a farkon ranar da aka ajiye shi, da kuma farkon ranar da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fara zama a kansa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika zuwa ga wance - wata mace daga Mutanen Madina -Sahlu ya ambace ta -; "Ki umarci yaronki kafinta ya haɗa min katakwaa da zan zauna a kansu idan zanyiwa mutane magana". Sai ta umarce shi sai ya yisu daga bishiyoyin daji, sannan ya zo da su, sai ta aika zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya yi umarni aka ajiyesu a nan, sannan na ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a kansu ya yi kabbara alhali yana kansu, sannan ya yi ruku'u alahali yana kansu, sannan ya sauko da baya, sai ya yi sujjada a asalin minbarin sannan ya dawo, yayin da ya gama sai ya fuskanci mutane sai ya ce: "ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi