Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

12 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Cewa wani mutum daga cikin Yahudawa ya ce masa: Yakai sarkin muminai, Wata aya a cikin littafinku kuna karantata, da a ce agurinmu mu Yahudawa ta sauka da mun riƙi ranar idi, ya ce: Wacce aya ce? ya ce: {A yau ne na cika muku Addininku kuma na cika muku ni'imata kuma na yardar muku da Musulunci a matsayin Addini} [al-Ma'ida: 3] Umar ya ce: Haƙiƙa mun san wannan ranar, da gurin da ta sauka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa alhali shi yana tsaye a Arfa a ranar Juma'a.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Allah - maɗaukakin sarki Ya ce: Na raba sallah tsakanina da tsakanin bawaNa gida biyu, bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan bawa ya ce: {Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: bawaNa ya godemin, idan ya ce: {Mai kyauta a duniya mai jin ƙan muminai a lahira}, Allah - Maɗaukakin sarki - zai ce: BawaNa ya yabeni, idan ya ce: {Mamallakin ranar sakayya}, Zai ce: BawaNa ya girmamaNi, - wani lokaci kuma ya ce: bawaNa ya fawwala (al'amuransa) gareNi -, idan ya ce: {Kai kaɗai muke bautawa, kuma gareka kaɗai muke neman taimako}, sai Ya ce: Wannan tsakanina da tsakanin bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa, idan ya ce: {ka shiryar da mu hanya madaidaiciya, hanyar waɗanda Ka yi ni'ima a garesu ba waɗanda Ka yi fushi a kansu ba, ba kuma ɓatattu ba}, zai ce: Wannan ga bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roƙa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«‌Yayin da (Mala’ika) Jibrilu yake zaune a wurin Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wata ƙara daga samansa, sai ya ɗaga kansa sama, sai ya ce: Wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, ba'a taɓa buɗe ta ba sai yau, sai wani Mala'ika ya sauko daga cikinta, sai ya ce: Wannan wani Mala'ika ne da ya sauko ƙasa, kuma bai taɓa sakkowa ba sai yau, sai ya yi sallama, ya ce: Ka yi albishir da haske biyu da aka ba ka su, wanda ba'a bawa wani Annabi kafinka ba; Ita ce Fatihatul Kitab, da ƙarshen suratul Baƙarah, ba za ka karanta wani harafi daga cikinsu ba sai an ba ka shi».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Ya kai baban Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare da kai?" ya ce: Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani. Ya ce: "Yakai baban Al-Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare dakai?" ya ce: Na ce; {Allah wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi Rayayye Tabbatacce da kanSa} [Al-Baqara: 255]. Ya ce: Sai ya daki kirjina, ya ce: "Wallahi ilimi ya faranta maka kai baban Al-Munzir".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wa shinfidarsa kowanne dare yana taro tafikansa, sannan ya yi tofi a cikin su, sai ya karanta a cikinsu: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadi }, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane} (Kul huwa da Falaki da kuma Nasi), Sannan ya shafi abinda ya yi wu daga jikinsa, yana farawa ne da su daga kansa da fuskarsa da abinda ya yi gaba na jikinsa, yanayin haka sau uku.
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
Lokacin da (ayar): {Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne, idan kun bayyanar da abin da ke cikin ranku ko kuka ɓoyeshi Allah zai yi muku hisabi da shi, Yana gafartawa wanda Ya so kuma Yana azabtar da wanda Ya so, Allah Mai iko ne akan dukkan komai}. [al-Baƙara: 284] ta sauka, ya ce: Sai hakan ya tsananta ga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - , sai suka zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sannan suka durƙusa akan gwiwowinsu, sai suka ce: Ya Manzon Allah, an ɗora mana ayyukan da zamu iya, sallah da azimi da jihadi da sadaka, haƙiƙa an saukar maka wannan ayar kuma ba zamu iyata ba, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Shin kuna son ku faɗi kamar yadda mazowa littafi biyu a gabaninku suka faɗa, mun ji mun saɓa?a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa», suka ce: Mun ji kuma mun bi ya Ubangijinmu gafararKa muke nema makoma tana wurinKa, lokacin da mutane suka karantata, sai harsunansu suka horu da ita, a bayanta sai Allah Ya saukar da {Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa haka ma muminai, kowannensu ya yi imani da Allah da mala'ikunSa da littattafanSa da ManzanninSa bama banbanta wani daga cikin ManzanninSa, suka ce: Mun ji mun bi ya Ubangijinmu gafararKa muke nema makoma tana wurinKa}. [al-Baƙara: 285], lokacin da suka aikata hakan sai Allah Ya shafe ta, sai ya saukar da {Allah ba Ya ɗorawa wata rai sai abin da zata iya, abin da ta aikata nata ne, haka abin da ta aikata na laifi yana kanta, ya Ubangijinmu kada Ka kamamu idan muka yi kuskure ko muka manta} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh» {Ya Ubangijnmu kada Ka ɗora mana wani nauyi kamar yadda ka ɗorawa waɗanda ke gabanmu} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh», {Ya Ubangijinmu kada ka ɗora mana abin da bazamu iya ba} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh», {Ka yi mana rangwami Ka gafarta mana Kajiƙanmu Ka taimakemu akan mutane kafirai} [al-Baƙara: 286].
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi