عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Rukunoni
Rukunoni (14)
Darajar hadisi
An ruwaito a
Nuna sauran majiyoyi
Mai ruwaya
Nuna duk masu ruwaya (79)
Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Wanda ya ce lokacin da ya ji mai kiran sallah: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, baShi da abokin tarayya, kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, na yadda da Allah Shi ne Ubangiji kuma (Annabi) Muhammad Manzo ne, kuma Musulunci shi ne Addini.
Za’a gafarta masa zunubinsa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Cewa Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo, sai ya yi sallah, sannan (ya zo) ya yi sallama ga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi-sai ya amsa masa kuma ya ce: Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba", sai ya koma ya yi sallah kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo ya yi sallama ga-Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Koma ka yi sallah, domin cewa kai baka yi sallah ba" sau uku, sai ya ce: Na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan iya yin wacce ta fita ba, to ka koya mini, sai ya ce:
"Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbara, sannan ka karanta abinda ya sawwaka tare da kai na Alkur'ani, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, sannan ka dago har sai ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, sannan ka dago har sai ka natsu a zaune, kuma ka aikata hakan acikin sallarka gaba dayanta".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimin da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah sau talatin da uku, ya yi wa Allah Kabbara sau talatin da uku, wancan (lissafin) shi ne casa'in da tara kenan, kuma yace a cikon ɗarin: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki ya tabbata gareShi, godiya ta tabbata gareShi, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai), za'a gafarta masa kurakuran sa, ko da sun kasance tamkar kumfar kogi".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta
{قل يأيها الكافرون} da {قل هو الله أحد}
a raka'o'i biyu (kafin sallar) Asuba.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikinmu, daga kowane ƙaramin (yaro) da babba, ɗa ne ko bawa, Sa’i na abinci, ko Sa’i na cukwi, ko Sa’i na sha'ir, ko Sa’i na dabino, ko Sa’i na zabibi, kuma bamu gushe ba muna fitar da shi har saida Mu'awiya ɗan Abu Sufyan - Allah Ya yarda da shi - ya gabato gurinmu yana mai aikin Hajji, ko yana mai Umarah sai ya yi wa mutane magana akan minbari, ya kasance daga abinda ya yi wa mutane magana da shi cewa ya ce: Lallai ni na ga cewa mudu biyu na alkamar Sham, sun yi daidai da sa'i ɗaya na dabino, sai mutane suka yi riko da hakan, Abu sa'id ya ce: Ammma ni ba zan gushe ba ina fitar da shi kamar yadda na kasance ina fitar da shi, muddin dai na rayu har abada.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi