Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

5 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Wanda ya zo muku alhali al'amarinku gabaɗaya yana hannun mutum ɗaya (kanku a haɗe a ƙarƙashin shugabancin mutum ɗaya), kuma yana son ya tsaga sandarku, ko ya raba jama'arku, to, ku kashe shi ".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Lallai za'a samu wasu fitintinu, ku saurara sannan a samu wasu fitintinu wanda ke zaune a cikinsu ya fi wanda ke tafiya a cikinsu, mai tafiya ya fi wanda ke gaggawa zuwa garesu, ku saurara idan suka sauka ko suka faru wanda yake da raƙuma to ya riski raƙumansa, wanda yake da tumakai to ya riski tumakansa, wanda yake da wata ƙasa to ya risku da ƙasarsa», ya ce sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah to kana ganin wanda ba shi da raƙuma ko tumakai ko ƙasa fa? ya ce: «Ɗayanku ya nufi takobinsa sai ya caka tsinin takobin a dutse, sannan ya tsira idan zai iya tsira, ya Allah shin na isar? ya Allah shin na isar?». Ya ce: sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah shin kana ganin idan aka tilastani har aka tafi da ni zuwa daya daga jama'a biyun, ko daya daga bangarori biyun, sai wani mutum ya dakeni da takobinsa, ko wata kibiya ta zo sai ta kasheni? ya ce: "Zai koma da zunubinsa da kuma zunubinka, kuma ya zama daga 'yan wuta".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Za'a samu wasu shugabanni zaku sansu kuma zaku yi inkarinsu, wanda ya sani ya kubuta, wanda kuma ya yi inkari ya kubuta, saidai wanda ya yarda ya kuma bi" suka ce: Shin ba ma yakesu ba? ya ce: "A'a, muddin dai suna sallah".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mubaya'a a kan ji da biyayya a halin rintsi da sauƙi, da farin ciki da baƙin ciki, da kuma nuna fifiko a kammu. Kuma kada mu yi wa ma'abota al'amari jayayya, kuma mu faɗi gaskiya a duk inda muke, ka da mu ji tsoron zargin mai zargi a al'amarin Allah.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a sai ya mutu, to, ya mutu irin mutuwar Jahiliyya, wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin makauniyar tuta, yana fushi saboda ƙabilanci, ko yake kira zuwa ƙabilanci, ko yake taimakon ƙabilanci, sai aka kashe shi, to, kisa ne na Jahiliyya, wanda ya yi fito na fito da al'ummata yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kiyaye wa tsakanin mumininta, kuma ba ya cika alkawari ga ma'abocin alkawari (kafirin amana), to, wannan ba ya tare da ni, ni ma ba na tare da shi".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi