Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

3 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tura wani mutum akan Zakkar Banu Sulaim, ana kiransa Ibnul Lutbiyyah, lokacin da ya zo sai ya yi masa lissafi, sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyauta ce. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Shin me yasa ba zaka zauna a cikin gidan babanka da babarka ba, har kyautar taka ta zo maka, idan kai mai gaskiya ne». Sannan ya yi mana huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi maSa yabo, sannan ya ce: «‌Bayan haka, lallai cewa ni ina ɗorawa mutum daga cikinku wani aiki daga abinda Allah Ya jiɓinta mini, sai ya zo sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyautar da aka bani ce, shin yanzu ba ya zauna a gidan babansa da babarsa ba har sai kyautar tasa ta zo masa !, Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar lahira, lallai cewa na san wani daga cikinku ya gamu da Allah yana ɗauke da raƙuminsa yana kuka, ko saniya tana kuka, ko akuya yana kuka» Sannan ya ɗaga hannunsa har sai da aka ga farin hammatarsa, yana cewa: «‌Ya Allah shin na isar ?» Ganin idona da kuma jin kunnena.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Dukkaninku masu kiwone to abin tambayane daga abinda yake kiwonta, shugaban mutane mai kiwo ne shi abin tambayane game da su, mutum mai kiwone ga iyalan gidansa kuma shi abin tambaya ne game da su, mace mai kiwo ce a dakin mijinta da ’yayansa kuma ita abar tambaya ce game da su,, bawa mai kiwo ne akan dukiyar shugabansa shi abin tambaya ne game da ita, ku saurara dukkaninku abin tambaya ne game da abin da aka ba shi kiwonsa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Za'a samu babakere da wasu al'amuran da zaku kisu" suka ce : Ya Manzon Allah mezaka umarcemu? Ya ce: "Ku bada hakkin da ya wajaba akanku, kuma ku roki Allah hakkinku ".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi