Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

7 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zauna wata rana akan minbari muma muka zauna a gefensa, sai ya ce: "Lallai ni ina jiye muku tsoro a baya na, abinda za'a buɗe muku na ƙawar duniya da adonta" sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, shin alheri yana zuwa da sharri ne? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shiru, sai akace masa: Meke damunka ne? kana yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma bai kulaka ba ? sai mukaga cewa can ana saukar me (da wahayi) ne? ya ce: Sai ya shafe gumi daga gare shi , sai ya ce: "Ina mai tambaya?" kamar shi ya yabe shi , sai ya ce: "Lallai alheri ba ya zuwa da sharri, yana daga abinda kaka take tsirarwa (akwai) abinda yake kashewa ko ya aibata, sai masu cin ciyayi, sun ci har saida kwiɓinansu suka cika sai suka fuskanci idan rana, sai suka yi toroso suka yi fitsari, suka yi kiwo, lallai wannan dukiyar koriyace mai zaƙi, madalla da na musulmi abinda aka bawa miskini daga gareta da maraya da ɗan matafiyi - ko kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata ya ce -: Kuma cewa shi wanda ya ɗauketa ba tare da haƙƙinta ba, to kwatankwacinsa kamar wanda yake ci ne ba ya ƙoshi, zata zama mai yi masa shaida ranar alƙiyama".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Zuciyar babba ba zata gushe ba tana budurwa a kan abubuwa biyu: A son duniya da tsawon buri".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
«Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Ya Allah babu wata rayuwa sai rayuwar lahira, ka gafartawa Mutanen Madina da waɗanda suka yi hijira».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na roki Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya bani, sannan na sake rokonsa sai ya bani, sannan ya ce da ni: «Ya Hakim lallai ita wannan dukiyar koriya ce mai zaƙi, wanda ya karɓeta da wadatar rai, za’a yi masa albarka a cikinta, wanda ya karɓeta da ɗaukakar rai ba za’a yi masa albarka a cikinta ba, sai ya zama kamar wanda yake ci ne ba ya ƙoshi, hannu maɗaukaki shi ne mafi alheri daga hannu maƙasƙanci». Hakim ya ce: Sai na ce: Ya Manzon Allah, na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan taɓa tauye wa wani, wani abu ba a bayanka har na bar duniya, Abubakar ya kasance yana kiran Hakim dan ya bashi kyauta (daga Baitul mali), sai ya ƙi karɓar komai daga gurinsa, sannan Umar ya kira shi dan ya ba shi, sai ya ƙi karɓa, sai ya ce: Yaku jama'a musulmai, lallai cewa ni ina ba shi haƙƙinsa wanda Allah Ya raba masa daga wannan ganimar, sai ya ƙi karɓarsa, Hakim bai tauyewa wani mutum daga cikin mutane ba bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - har sai da ya rasu - Allah ya yi masa rahama -.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai wasu mutane suna kutsawa a dukiyar Allah ba tare da wani haƙƙi ba, to, wuta ta tabbata a garesu ranar al-ƙiyama".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
Shimfiɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance ta jemammiyar fata ce, cikinta kaba ne, a Riwayar Muslim kuma : Matashin kai na Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wanda yake dogara a kan shi ya kasance na jemammiyar fata ne, cikinta kaba ce.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi