Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

5 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu"
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka ruwaito, wannan lafazin na Muslim ne, amma Bukhari ya rawaito shi a taƙaice.
التصنيف الشرعيهدي النبي صلى الله عليه وسلم في الذكر، الأدعية المأثورة
Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيأنواع الدعاء، الأدعية المأثورةموضوعات الحديثالدعاء
"Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena da wautata, da wuce gona da irina a cikin dukkan al'amarina, da abinda Kaine Mafi sani da shi daga gareni, ya Allah Ka gafarta mini kurakuraina, da gangancina da jahilcina da kakacina, dukkan hakan daga garenin ne, ya Allah Ka gafarta mini abinda na gabatar da abinda na jinkirtar, da abinda na ɓoye da abinda na bayyana, kaine Mai gabatarwa kuma Kaine Mai jinkirtarwa, kuma kaine Mai iko akan dukkan komai".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيالأدعية المأثورة
Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيآداب العالم والمتعلم، الأدعية المأثورة، أذكار الصلاةموضوعات الحديثحقوق النبي ﷺ، صفة الصلاة
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yin addu'a yana cewa: "Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)". A cikin wani lafazin na Muslim: "Idan dayanku ya gama tahiyar karshe, to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa hudu: Daga azabar kabari, da fitinar rayuwa da mutuwa, da sharrin Mai yawan yawo makaryaci (Jujal).
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيالأدعية المأثورة، أذكار الصلاةموضوعات الحديثالدعاء، أشراط الساعة، سنن الصلاة، صفة الصلاة