عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Rukunoni
Darajar hadisi
An ruwaito a
Nuna sauran majiyoyi
Mai ruwaya
Nuna duk masu ruwaya (34)
«Haƙiƙa ka yi tambaya game da wani abu mai girma, kuma cewa shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa ka bautawa Allah kada ka hada shi da kowa, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azumci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin (Allah).
Sannan ya ce: Shin ba zan shiryar da kai zuwa ga ƙofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaka tana shafe zunubi kamar yadda ruwa yake kashe wuta, da kuma sallar mutum a tsakiyar dare, sannan ya karanta: {Sasanninsu suna nisantar makwanci} har ya kai (suna aikatawa).
sannan ya ce: Shin bana baka labari da asalin al'amari ba da ginshiƙinsa da kuma ƙololuwar tozansa, sai na ce: Na'am ya Manzon Allah, ya ce: Asalin al'amari shi ne Musulunci, ginshiƙinsa ita ce sallah, kuma ƙololuwar tozansa shi ne jihadi.
Sannan ya ce: Shin bana baka labari ba da abinda zai haɗa haka gaba ɗaya ba? na ce: Na'am ya Manzon Allah! Sai ya riƙe harshensa kuma ya ce: Ka riƙe wannan, na ce: Ya Annabin Allah! Muma za’a kama mu da abin da muke magana da shi? sai ya ce: Babarka ta yi wabinka ! ai ba wani abu ne yake afkar da mutane ta fuskokinsu ko ta hancinsu ba sai abin da harsunansu suke girba».
Ingantacce ne Tirmizi ne ya ruwaito shi
"Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya faɗi alheri ko ya yi shiru, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama maƙocinsa, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama baƙonsa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai cewa wani mutum ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Yi min wasiyya, sai ya ce: "Kada ka yi fushi" sai ya maimata da yawa, ya ce: "Kada ka yi fushi".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
«Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa».
Nawawi ya ce: Hadisi ne mai kyau Ibnu Majah da Baihaki da wasun su ne suka ruwaito shi
«Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga cikin abubuwa uku, bazawarin da ya yi zina, da ran (da ya kashe) rai, da wanda ya bar addininsa wanda ya bar jama'a».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Babu cuta ba cutarwa».
Hasan ne Ibnu Majah da Darakutni da wasunsu Suka ruwaito shi a matsayin Musnad.
«Dukkan ayyuka basa yi yiwuwa sai da niyyoyi, kuma kowanne mutum yana da ladan abin da ya niyyata ne wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da ManzonSa to hijirarsa tana ga Allah da ManzonSa, wanda hijirarsa ta kasance dan duniya da zai sameta ko wata mace da zai aureta to hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gare shi».
Ingantacce ne Limaman Malaman Hadisi guda biyu ne suka rawaito shi, Abu Abdullahi Muhammad bn Isma'il bn Ibrahim bn al-Mughirah bn Bardizbah al-Bukhari, da Abul Husain Muslim bn al-Hajjaj bn Muslim al-Kushairi an-Naisaburi, a cikin Sahihansu guda biyu, waɗanda su ne mafi ingancin littattafan da aka wallafa.
"An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi