Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

29 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Addini nasiha ne" Muka ce; ga wa? Ya ce; "Ga Allah da littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmai da dukkaninsu".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Shayarwa tana haramta dukkan abin da haihuwa take haramtawa».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Tsarki rabin imani ne, kuma (faɗin) godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (faɗin) tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da ƙasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, haƙuri haskene, Alƙur’ani hujjane gareka ko a kanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto shi ko kuma ya halakar da shi».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Da a ce ana bawa mutane abu saboda iƙirarin cewa nasu ne, da da yawa daga cikin mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanansu, sai dai wanda duk ya yi da'awa to shi zai zo da shaidu, kuma rantsuwa tana kan wanda ya musanta».
Hasan ne Baihaki da wasu suka ruwaito shi kamar haka, kuma sashensa yana cikin Bukhari da Muslim.
"Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya faɗi alheri ko ya yi shiru, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama maƙocinsa, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama baƙonsa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga cikin abubuwa uku, bazawarin da ya yi zina, da ran (da ya kashe) rai, da wanda ya bar addininsa wanda ya bar jama'a».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi