Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

20 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Lallai cewa wani mutum ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Yi min wasiyya, sai ya ce: "Kada ka yi fushi" sai ya maimata da yawa, ya ce: "Kada ka yi fushi".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
«Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga cikin abubuwa uku, bazawarin da ya yi zina, da ran (da ya kashe) rai, da wanda ya bar addininsa wanda ya bar jama'a».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Dukkan ayyuka basa yi yiwuwa sai da niyyoyi, kuma kowanne mutum yana da ladan abin da ya niyyata ne wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da ManzonSa to hijirarsa tana ga Allah da ManzonSa, wanda hijirarsa ta kasance dan duniya da zai sameta ko wata mace da zai aureta to hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gare shi».
Ingantacce ne Limaman Malaman Hadisi guda biyu ne suka rawaito shi, Abu Abdullahi Muhammad bn Isma'il bn Ibrahim bn al-Mughirah bn Bardizbah al-Bukhari, da Abul Husain Muslim bn al-Hajjaj bn Muslim al-Kushairi an-Naisaburi, a cikin Sahihansu guda biyu, waɗanda su ne mafi ingancin littattafan da aka wallafa.
"An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi
"An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka, idan suka aikata hakan sun tsare jinanensu da dukiyoyinsu daga gareni sai dai da hakkin Musulunci, kuma hisabinsu yana ga Allah".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Duk abin da na haneku daga gare shi to ku nisance shi, kuma abinda na umarce ku da shi to ku zo da shi dai dai iyawarku, domin abin da ya halaka magabatanku (shi ne) yawan tambayoyinsu da kuma saɓawarsu ga Annabawansu».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi
"Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Dukkanin gaɓa ta mutane sadaka ce gare shi, kowanne yinin da rana ta hudu a cikinsa ka daidaita tsakanin mutum biyu sadaka ne, ka taimaki mutum a dabbarsa ka ɗora shi a kanta ko ka sauke masa kayansa daga kanta to sadaka ne, kalma mai daɗi sadaka ce, dukkanin takun da ka yi zuwa masallaci sadaka ne, ka kauda ƙazanta akan hanya sadaka ne».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi