Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

6 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - zuwa Aljanna, sai ya ce: ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta sai ya dawo, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa wani daya ba zai ji ta ba sai ya shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan ki, sai Ya ce; Tafi zuwa gareta ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga ta an kewayeta da abubuwan ki, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa shiga cikinta . Ya ce: Tafi ka yi duba zuwaga wuta da kuma abinda na tanada ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga shashininta yana hawa kan sashi, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa ba wanda zai shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan sha'awa , sai ya ce; ka koma ka yi duba zuwa gareta, sai ya yi duba zuwa gareta sai ga shi ita kuma an kewayeta da abubuwan sha’awa, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa tsira daga gareta a ce bai shigeta".
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi
Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - ya ce:Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kwaɗayi gareni zan gafarta maka abinda ya kasance gareka babu ruwaNa. Ya kai ɗan Adam da zunubanka sun kai ƙololuwar sama, sannan ka nemi gafarata zan gafarta maka, babu ruwaNa. Ya kai ɗan Adam lallai cewa kai da ka zo min da kurakurai cikin ƙasa sannan ka gamu dani ba yi min tarayya da wani abu ba, da na zo maka da gafara cikinta".
Hasan ne Tirmizi ne ya ruwaito shi
"Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)".
Hasan ne Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad
Yayin da (aya) ta sauka {Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima} [Al-Takasur: 8], sai Zubair ya ce: Ya Manzon Allah, shin wace ni'ima ce za a tambayemu game da ita, bakake biyu ba ne kaɗai; dabino da ruwa? sai ya ce: "lallai dai kam daa sannu zai kasance".
Hasan ne Tirmizi ne ya Rawaito shi
"Wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cutar, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawar".
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
"Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi".
Hasan ne Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi