Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

21 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu, sai ya ce: "Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci" Sannan ya dauki wani danyan itacan dabino, sai ya raba shi biyu, sai ya kafa daya a kowanne kabari, suka ce: Ya Manzon Allah, meyasa ka aikata hakan, sai ya ce: "Watakila a saukaka musu muddin dai basu bushe ba".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai Shaiɗan haƙiƙa ya yanke ƙaunar masu sallah su bauta masa a tsibirin larabawa, sai dai a sa gaba a tsakaninsu".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi a cikin Mukaddima din sa
Ma’aikin Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya hana askin banza [barin wani wuri a kai da ba a aske ba].
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi