Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

47 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa.
Hasan ne Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad
An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u", kuma an tambayeshi game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane wuta sai ya ce: "Baki da farji".
Hasan ne kuma Ingantacce Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
«Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi, ka ɗabi'anci mutane da kyawawan ɗabi'u».
Tirmizi ya ce Hadisi ne Hasan Tirmizi ne ya ruwaito shi
"Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Wani mutum ya kasance yana bawa mutane bashi, ya kasance yana cewa wani yaronsa: Idan kaje wurin wanda ke cikin muwuyacin hali to ka kau da kai gare shi , muna fatan Allah ya ketare mana (zunubanmu), sai ya gamu da Allah sai Ya yafe masa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace».
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.