Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

5 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيفضل الذكر، الأذكار المطلقةموضوعات الحديثالذِّكْر، سعة فضل الله عز وجل
Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيفضل الذكر، فوائد ذكر الله عز وجل، الأذكار المطلقةموضوعات الحديثالذِّكْر، سعة فضل الله عز وجل
«‌Wanda ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki naSa ne, godiya taSa ce, kuma Shi Mai iko ne a kan dukkan komai) sau ɗari a cikin yini, yana da abinda ya yi daidai da wuyaye goma, kuma za'a rubuta masa kyakkyawa ɗari, kuma za'a shafe masa mummuna ɗari, kuma za ta kasance tsari daga Shaiɗan a wannan yinin nasa, har sai ya kai maraice, kuma ba wanda zai zo da abin da ya fi wanda ya zo da shi, saidai wanda ya aikata sama da hakan».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيفضل الذكر، فوائد ذكر الله عز وجل
"Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيفضل الذكر، الأذان والإقامةموضوعات الحديثأحكام الأذان والإقامة
Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, mulki na sa ne, godiya ta sa ce, Shi mai iko ne a kan komai. Sau goma . zai kasance kamar wanda ya ‘yanta mutane huɗu daga tsatsan (Annabi) Isma’il.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيفضل الذكر، الأذكار المطلقةموضوعات الحديثالذِّكْر