Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

13 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Wata miskiniya ta zo wurina tana ɗauke da 'ya'yanta mata biyu, sai na ciyar da ita dabinai uku, sai ta ba wa kowacce ɗaya daga cikinsu su biyun dabinon, sai ta ɗaga dabino zuwa bakinta don ta ci, sai 'ya'yan na ta mata biyun suka nemi ƙara ci daga gareta, sai ta raba musu dabinon da ta so ta ci a tsakaninsu, sai sha'anin ta ya ƙayatar da ni, sai na gaya wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - abin da ta aikata, sai ya ce: «‌Lallai haƙiƙa Allah Ya wajabta mata Aljanna da shi, ko kuma Ya 'yanta ta daga wuta da shi».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Wanda ya reni 'yan mata biyu har suka balaga zai zo ranar alƙiyama ni da shi" sai ya dunƙule yatsunsa.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakurai da shi ba, kuma Yake ɗaukaka darajoji da shi?" Suka ce: Na'am, ya Manzon Allah, ya ce: "Cika alwala a lokutan da ake ƙi, da yawan takawa zuwa masallatai, da jiran sallah bayan sallah, wadannan su ne shi ne zaman dako".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Wata rana wani mutum yana tafiya a wata hanya, sai ya samu reshen wata ƙaya a kan hanyar, sai ya kawar da shi, sai Allah Ya yaba masa Ya kuma gafarta masa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, kuma bigiren bulalar ɗayanku a aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, yammacin da bawa zai yi shi saboda Allah ko jijjifi shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Mafificin dinaren (kudi) da mutum zai ciyar da shi: Dinarin da ya ciyar da shi ga iyalansa, da dinaren da mutum yake ciyar da shi ga dabbarsa a tafarkin Allah, da dinaren da yake ciyar da shi ga abokansa a tafarkin Allah" Abu Kilaba ya ce: "Sai ya fara da iyali, sannan Abu Kilaba ya ce: Kuma wanne mutum ne mafi girman lada kamar mutumin da yake ciyar da iyali ƙanana don ya rufa musu asiri ko Allah Ya anfanar da su da shi, kuma ya wadata su".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci, Yana ƙasa da ma'auni kuma Yana ɗaga shi, ana ɗaga aikin dare kafin aikin rana zuwa gare Shi, da aikin rana kafin aikin dare, shamakinSa shi ne haske, da ace zai yaye shi da hasken fuskarSa ya ƙona inda ganinsa ya tiƙe daga halittarSa».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi