Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

75 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Dukkan ayyuka (ba sa inganta) sai da niyya, kaɗai mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne, wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da manzonsa, to, hijirarsa tana ga Allah da manzonsa, wanda hijirarsa ta kasance don duniya da zai sameta, ko wata mace da zai aureta, to, hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gareshi". A wani lafazin na Bukhari; "Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyyoyi, kaɗai kowane mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na gani yau ba na alheri da sharri, da kun san abinda na sani da kun yi dariya kaɗan kuma kun yi kuka da yawa" ya ce: Babu wani yini da ya taɓa zowa sahabban manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mafi tsanani kamar wannan yinin, ya ce: Sai suka rufe kawunansu suna ruri, ya ce: Sai Umar ya miƙe sai ya ce: Mun yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin annabi, ya ce: Sai wani mutum ya miƙe sai ya ce: Waye babana? ya ce: "Babanka shi ne wane", sai wannan ayar ta sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku tambayi wasu abubuwa idan suka bayyana gareku zasu munana muku}. [al-Ma'ida: 101].
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basu taɓa ƙoshi daga abincin alkama a darare uku ajere ba tunda ya zo Madina, har aka karɓi ransa.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa, kuma yana daga bayyanarwa mutum ya aikata wani aiki (mummuna) da daddare, sannan ya wayi gari Allah Ya rufa masa asiri, sai ya ce: Ya (ya falalarsa kansa) wane, jiya da daddare na aikata kaza da kaza, alhali ya kwana Uabangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lalle ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yana shimfiɗa hannunSa da daddare domin mai laifi da rana ya tuba, kuma Yana shimfiɗa hannunSa da rana domin mai laifi da daddare ya tuba, har sai rana ta ɓullo daga yammacinta".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ce: Na tanadarwa bayiNa na gari, abinda wani ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, kuma bai taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani ɗan Adam ba» Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Wata rai ba ta sanin abinda aka ɓoye musu na abinda rai yake farin ciki da shi} [al-Sajdah: 17].
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yayin da ya ji wata kara, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin kun san mene ne wannan?" ya ce: Muka ce: Allah da ManzonSa ne mafi sani, ya ce: "Wannan wani dutsene da aka jefa shi cikin wuta tun shekara saba'in, shi (dutsan) yana faɗawa cikin wuta a yanzu, har sai da ya kai karshanta".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, hakan zai sa (ku godewa Allah) ba za ku raina ni’imominSa gareku ba».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi