Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

75 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan surar wata daren goma sha huɗu, sannan masu biye musu akan surar tauraro mafi tsananin haske, ba sa fitsari ba sa bahaya, ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abin taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski, kuma abin kunna tiraren wutarsu shi ne icen tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inun (Masu tsananin farin ido da tsananin ƙwayar baƙin da ke cikin idon), suna a kan halittar mutum ɗaya, akan surar babansu (Annabi) Adam, zira'i sittin a cikin sama».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta", sai na ce: Ya Manzon Allah, wannan mai kisan ne, to, mene ne laifin wanda aka kashe? ya ce: "Lallai shi ma ya kasance mai kwaɗayi ne a kan kashe ɗan uwansa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Ni ne mafi wadatar abokanan tarayya daga shirka, duk wanda ya aikata wani aiki ya hada ni da wani a aikin to Zan bar shi da shirkarsa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Shin baku kasance kuna yadda kuka so a cikin abin ci da abin sha ba? Haƙiƙa na ga Annabinku - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali bai samu dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi ba.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«‌Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai, har kada wani ya yi wa wani alfahari, kuma kada wani ya zalinci wani».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi