عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Rukunoni
Darajar hadisi
An ruwaito a
Nuna sauran majiyoyi
Mai ruwaya
Nuna duk masu ruwaya (66)
"Idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, ya ce: Allah -Maɗaukakin sarki - zai ce: Kuna son wani abu ne da zan ƙaro muku shi? sai su ce: Ba Ka haskaka fusokinmu ba? kuma ba Ka shigar da mu aljannah ba, kuma Ka tseratar da mu daga wuta? ya ce: Sai a yaye hijabi, ba'a basu wani abu mafi soyuwa a gare su ba daga duba zuwa Ubanginsu - Mai girma da ɗaukaka -".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Za'a bijiro da fitintinu akan zukata kamar tabarma kara-kara, duk zuciyar da aka cakuɗata da su sai ta yi masa baƙin ɗigo, duk zuciyar data musantasu kuwa za’a yi mata farin ɗigo, har su zama akan zukata biyu (nau'i biyu), akan farar zuciya kwatankwacin fal dutse, to wannan fitinar ba zata cutar da ita ba muddin sammai da ƙasa suna nan, ɗayar kuma baƙace ƙirin kamar kifaffiyar ƙwarya, ba ta san wani aikin alheri, kuma bata inkarin wani abin ƙi, sai abinda aka cakuɗa mata na son ranta". Huzaifa ya ce: Kuma na zantar da shi, cewa lallai tsakaninka da su akwai wata kullalliyar ƙofa ta kusa a karya ta, Umar ya ce: Shin karyawa za'a yi kaicanka? Inama dai bude ta za'a yi watakila a dawo da ita, na ce: Kuma na zantar da shi wani labarin da bana galadi ba cewa wannan kofar wani mutum ne da za'a kashe ko ya mutu.
Abu Khalida ya ce: Sai na ce wa Sa'ad: Ya Abu Malik, me ake nufi da Aswad Murbadun? Ya ce: Tsananin fari a cikin baki. Ya ce: Sai na ce: To me ake nufi da al-Kuzul mujakkhiya? ya ce: Wacce aka kife.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Lallai a cikin aljanna akwai wata kasuwar da 'yan aljanna suke zuwanta kowacce Jumu'a, sai iskar arewa ta taso sai ta watsu a fuskokinsu da tufafinsu, sai su ƙara kyau da ƙawa. sai su koma zuwa ga iyalansu alhali haƙiƙa sun ƙara kyau da ado, sai iyalansu suce musu: Wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ƙawa a bayanmu, sai su ce: Kuma wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ado a bayanmu".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".
Ingantacce ne Muslim da Ahmad ne suka rawaito shi
"Lallai wasu mutane suna kutsawa a dukiyar Allah ba tare da wani haƙƙi ba, to, wuta ta tabbata a garesu ranar al-ƙiyama".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi
"Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Dukkan ayyuka basa yi yiwuwa sai da niyyoyi, kuma kowanne mutum yana da ladan abin da ya niyyata ne wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da ManzonSa to hijirarsa tana ga Allah da ManzonSa, wanda hijirarsa ta kasance dan duniya da zai sameta ko wata mace da zai aureta to hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gare shi».
Ingantacce ne Limaman Malaman Hadisi guda biyu ne suka rawaito shi, Abu Abdullahi Muhammad bn Isma'il bn Ibrahim bn al-Mughirah bn Bardizbah al-Bukhari, da Abul Husain Muslim bn al-Hajjaj bn Muslim al-Kushairi an-Naisaburi, a cikin Sahihansu guda biyu, waɗanda su ne mafi ingancin littattafan da aka wallafa.