Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

110 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Wani balaraben kauye ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ka sanar maganar da zan fada, ya ce: "Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya, Allah ne Mafi girma Mai girma, godiya ta tabbata ga Allah mai yawa, tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, babu dabara babu karfi sai ga Allah Mabuwayi Gwani" sai ya ce: Wadannan na Ubangijina ne, to ni me gareni? ya ce: "Ka ce: Ya Allah Ka gafarta mini Ka ji kaina Ka shiryar dani Ka azurtani".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Ya ku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Ya ce: {Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}. [al-Mu'uminun: 51] . Kuma Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. [al:Baƙara: 172]. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama: Ya Ubangiji, ya Ubangiji, abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to tayaya za'a amsa masa ga hakan?".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ce: Na tanadarwa bayiNa na gari, abinda wani ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, kuma bai taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani ɗan Adam ba» Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Wata rai ba ta sanin abinda aka ɓoye musu na abinda rai yake farin ciki da shi} [al-Sajdah: 17].
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Masu biyewa juna mai fadinsu ba ya tabewa - ko mai aikata su - a bayan kowacce sallar farilla, Tasbihi talatin da uku, da Tahmidi talatin da uku, da Kabbara talatin da hudu".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yayin da ya ji wata kara, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin kun san mene ne wannan?" ya ce: Muka ce: Allah da ManzonSa ne mafi sani, ya ce: "Wannan wani dutsene da aka jefa shi cikin wuta tun shekara saba'in, shi (dutsan) yana faɗawa cikin wuta a yanzu, har sai da ya kai karshanta".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, hakan zai sa (ku godewa Allah) ba za ku raina ni’imominSa gareku ba».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«‌Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Lallai a cikin aljanna akwai wata bishiya mahayin doki horarre mai sauri zai yi tafiyar shekara ɗari ba zai iya wuceta ba".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi