Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

13 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Za'a ce da ma'abocin Alkur’ani: Karanta ka daukaka, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya, domin cewa matsayinka zai tasayane a karshen ayar da ka karantata".
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi.
التصنيف الشرعيوصف القرآن وفضائله، آداب تلاوة القرآن الكريم، صفات الجنة والنارموضوعات الحديثتلاوة القرآن، القرآن وعلومه، الإيمان باليوم الآخر
"Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".
Ingantacce ne Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
التصنيف الشرعيفضل العلم، آداب العالم والمتعلم
"Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shi
التصنيف الشرعيآداب اللباس
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin yin bacci yana sanya hannunsa ƙarƙashin kansa, sannan ya ce: «‌Ya Allah Ka kareni azabarKa ranar da zaKa tara ko zaka tashi bayinKa».
Ingantacce ne Tirmizi ne ya ruwaito shi
التصنيف الشرعيآداب النوم والاستيقاظ
"Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi.
التصنيف الشرعيالأخلاق الحميدة، آداب الكلام والصمتموضوعات الحديثالحب في الله والبغض في اللهمحاور التعريف بالإسلاممحاسن الأخلاق