Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

50 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wata tafiya, sai na sunkuyo don in cire masa huffi, sai ya ce: "Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki" sai ya yi shafa akansu.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin yin bacci yana sanya hannunsa ƙarƙashin kansa, sannan ya ce: «‌Ya Allah Ka kareni azabarKa ranar da zaKa tara ko zaka tashi bayinKa».
Ingantacce ne Tirmizi ne ya ruwaito shi
"Idan ɗayanku zai ci; to, ya ci da damansa, idan zai sha; to, ya sha da damansa, domin cewa Shaiɗan yana ci da hagunsa, kuma yana sha da hagunsa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Duk mutumin da ya cewa ɗan'uwansa: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya dawo da ita (ya lazimceta), idan ya zama kamar yadda ya ce ne, inba haka bafa to zata dawo kansa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Mayafin musulmi zuwa rabin ƙwauri ne, kuma babu laifi - ko babu zunubi - a tsakanin sa da idan sawu, kuma abinda ya zama ƙasa da idan sawu to shi yana cikin wuta, wanda ya ja mayafinsa (ƙasa) dan girman kai to Allah ba zai yi duba zuwa gareshi ba".
Ingantacce ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad.
«‌Wanda ya nemi sanin wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da shi ba ya nemansa sai dan ya samu wata haja ta duniya da shi ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙima» wato ƙanshinta.
Ingantacce ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad.
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce mu da abubuwa guda bakawai, kuma ya hanemu da abubuwa bakwai: Ya umarcemu da duba mara lafiya, da raka jana’iza, da gaida mai atishawa, da kuma kuɓutar da rantsuwa, ko mai rantsuwa, da taimakon wanda aka zalunta, da kuma amsawa mai gayyata, da yaɗa sallama. Ya kuma hana mu yin zobe - ko sanya zoben zinare, da sha acikin abin sha na azurfa, da al-Mayathir, (Shi ne matakalar abunda ake sanyawa a shinfidar doki) da al-ƙissi (zabon Masar, nau’i ne na alhariri mai kauri) da kuma sanya alharini, da al-Istabraƙ (Alharini mai kauri) Dibaj (shi ma nau’i ne na alharini mai kauri).
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi