Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

50 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Babu wani abu mafi nauyi a ma'aunin mumini a ranar Alkiyama daga kyawawan dabi'u, lallai Allah Yana kin mai alfasha mai mummunar magana".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi ne Suka Rawaito shi
"Babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu sannan su gaisa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu".
Ingantacce ne a baki dayan hanyoyin sa Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Cewa wani mutum a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sunansa Abdullahi, kuma ya kasance ana yi masa laƙabi da jaki, ya kasance yana sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dariya, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ya yi masa bulala saboda giya, sai aka zo da shi wata rana sai ya sa aka yi masa bulala, sai wani mutum daga cikin mutanen ya ce: Ya Allah Ka tsine masa, ina mamakin yawan abin da ake zuwa da shi saboda shi?! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku tsine masa, na rantse da Allah ban san wani abu daga gare shi ba sai dai yana son Allah da ManzonSa".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".
Ingantacce ne Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
"Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shi
"Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi ".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi