Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

50 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Allah ba Ya duba zuwa wanda ya ja tufansa (ƙasa) dan girman kai".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko dutse ya tsare tsakaninsu sannan ya haɗu da shi to ya yi masa sallama kuma".
Ingantacce ne Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Na ce: Ya Manzon Allah menene tsira? ya ce: "Ka mallaki harshenka gareka, kuma gidanka ya yalwaceka, ka yi kuka akan kuskurenka".
Ingantacce ne Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
"Mumini ba mai yawan suka bane ko mai yawan tsinuwa ba ko mai yawan alfasha ba ko mai zancen banza ba".
Ingantacce ne Tirmizi ne ya ruwaito shi
"Idan dayanku zai yi alwala to ya sanya ruwa a hancinsa sannan ya face, wanda zai yi tsarkin hoge to ya yi shi wutiri, idan dayanku ya farka daga baccinsa to ya wanke hannunsa kafin ya shigar da su a ruwan alwalarsa, domin cewa dayanku ba ya sanin a'ina hannunsa ya kasance". Lafazin Muslim: "Idan dayanku ya farka daga baccinsa kada ya nutsa hannunsa a cikin kwarya har sai ya wankesu sau uku, domin cewa shi ba ya sanin a'ina hannunsa ya sakance ".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Cewa wani mutum ya ci a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da hannun hagunsa, sai Ma’aikin Allah ce da shi: "Ka ci da hannun damanka ." Ya ce: Ba zan iya ba. Ya ce: "Ba za ko ka iya ba", ba abin da ya hana shi sai girman kai, ya ce: Bai kara daga shi zuwa bakinsa ba.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wa shinfidarsa kowanne dare yana taro tafikansa, sannan ya yi tofi a cikin su, sai ya karanta a cikinsu: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadi }, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane} (Kul huwa da Falaki da kuma Nasi), Sannan ya shafi abinda ya yi wu daga jikinsa, yana farawa ne da su daga kansa da fuskarsa da abinda ya yi gaba na jikinsa, yanayin haka sau uku.
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.