Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

73 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Yana daga abin da mutane suka riska daga zancen Annabci na farko: Idan ba ka da kunya, to ka aikata abin da kake so".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Babu wani abu mafi nauyi a ma'aunin mumini a ranar Alkiyama daga kyawawan dabi'u, lallai Allah Yana kin mai alfasha mai mummunar magana".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi ne Suka Rawaito shi
Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya faɗi alheri ko ya yi shiru, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama maƙocinsa, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya girmama baƙonsa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Bai kasance mai yawan alfasha ba, ko mai yawan ɗorawa kansa alfasha ba, ko mai kwararoto a kasuwa, kuma ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai yana yin afuwa kuma yana kau da kai.
Ingantacce ne Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
"Lallai cewa wani mutum ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Yi min wasiyya, sai ya ce: "Kada ka yi fushi" sai ya maimata da yawa, ya ce: "Kada ka yi fushi".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Shin bana baku labari ba da mafi alherinku daga mafi sharrinku?" Ya ce: Sai suka yi shiru, sai ya faɗi haka sau uku, sai wani mutum ya ce: Eh ya Manzon Allah, bamu labari da mafi alherinmu daga mafi sharrinmu, ya ce: "Mafi alherinku shine wanda ake fatan alherinsa kuma ake amincewa sharrinsa, kuma mafi sharrinku shine wanda ba'a fatan alherinsa kuma ba'a amincewa sharrinsa".
Ingantacce ne Tirmizi ne ya ruwaito shi