Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

34 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Na hore ku da gaskiya, saboda gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna, kuma mutum ba zai gushe ba yana yin gaskiya, kuma yana kirdadon gaskiya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan gaskiya ne. Kuma na haneku da ƙarya, saboda ƙarya tana shiryarwa ne zuwa ga fajirci, kuma fajirci yana shiryarwa ne zuwa ga wuta, mutum ba zai gushe ba yana yin ƙarya kuma yana kirdadon ƙarya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan ƙarya".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi ne wanda yake mallakar kansa a yayin fushi".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu, sai ya ce: "Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci" Sannan ya dauki wani danyan itacan dabino, sai ya raba shi biyu, sai ya kafa daya a kowanne kabari, suka ce: Ya Manzon Allah, meyasa ka aikata hakan, sai ya ce: "Watakila a saukaka musu muddin dai basu bushe ba".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Yana daga abin da mutane suka riska daga zancen Annabci na farko: Idan ba ka da kunya, to ka aikata abin da kake so".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ma’aikin Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya hana askin banza [barin wani wuri a kai da ba a aske ba].
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Allah Ya yi wa mutum rahama mai saukakawa idan zai siyar, kuma idan zai siya, kuma idan zai nemi biyan bashi".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.