Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

2 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Na kasance ina shayar da mutane ( giya) a gidan Abu Ɗalha, kuma giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, sai a (Cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yan dabino kafin su zama ɗanye) Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci wani mai kira ya yi kira: Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai ta kwaranya a lungunan Madina, sai wasu cikin mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe wasu mutane alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da: {Babu laifi ga waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka ɗanɗana} [al-Ma'ida: 93] karanta ayar har ƙarshenta.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na kasanace a wurin minbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai wani mutum ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai kawai in shayar da mai yin aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa, sai Umar ya yi musu tsawa, kuma ya ce: Kada ku ɗaga muryarku a wajen mimbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali ranar Juma'a ce, sai dai idan na sallaci Juma'a zan shiga in tambaye shi a cikin abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Shin yanzu kwa mayar da shayar da mai aikin Hajj da kuma raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira}[al-Taubah: 19] karanta ayar har zuwa ƙarshenta.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi