Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

10 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta, Babu azumi a ranaku biyu: Karamar sallah da babbar sallah, kuma babu sallah bayan asuba har sai rana ta bullo, kuma babu bayan la'asar har sai ta fadi, kuma ba'a daure sirdi (nikar gari domin tafiya) sai a masallatai uku: Masallaci mai alfarma, da masallacin Kudus, da masallacina wannan".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa wata mata daga mutanen Madina, Ibnu Abbas ya ambaceta sai na manta sunanta: "Meya hanaki ki yi Hajji tare da mu?" Ta ce: Ba mu da komai sai raƙuma biyu, sai baban ɗanta da ɗanta suka yi Hajji akan raƙumi ɗaya, kuma ya bar mana ɗayan muna ban ruwa da shi, ya ce: "Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan kwanakin". Wato kwanaki goman, (Zul Hijja) Suka ce: Ya Ma’aikin Allah, Har jihadi domin ɗaukaka addinin Allah ? Ya ce: Har Jihadi domin ɗaukaka addinin Allah, sai dai mutumin da ya fita da kansa da dukiyarsa, kuma bai dawo da komai ba.
Ingantacce ne Bukhari ne ya ruwaito shi, da Abu Dawud, kuma lafazin nasa ne.
Ya manzon Allah, muna ganin yaƙi shi ne mafificin aiki, shin ba ma yi yaƙi ba? ya ce: "A'a, sai dai mafificin yaƙi: Shi ne kubutaccen aikin Hajji".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
Cewa Talbiyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "AmsawarKa ya Allah, amsawarKa, amsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa, lallai cewa godiya da ni'ima na Ka ne kuma mulki ma naKa ne, baKa da abokin tarayya" Ya ce: Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya kasance yana ƙarawa a cikinta: AmsawarKa amsawarKa, da taimakonKa (akan aiki), alheri yana hannayenKa, amsawarKa fata yana gareKa da kuma aiki.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Cewa shi ya zo wurin Hajarul Aswad (Baƙin dutse) sai ya sumbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi