Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

18 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Cewa wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun ce wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya Manzon Allah, masu dukiyoyi sun tafi da ladaddaki, suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, suna azimi kamar yadda muke yin azumi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, ya ce: "Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne", Suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama yana da lada a cikinta? ya ce: "Shin kuna ganin da ace zai sanyata a cikin haram shin zai zama a kansa akwai zunubi a cikinsa? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su: Waye Muhammad a cikinku? alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide a tsakaninsu, sai muka ce : Wannan farin mutumin wanda ke kishingide. Sai mutumin ya ce da shi: Ya kai Dan Abdul Mudallib sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: "Hakika na amsa maka". Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji haushi na a ranka? sai ya ce: "Ka tambayi abinda ya bayyana gareka" sai ya ce: Ina tambayarka dan Ubangijinka da Ubangijin wadanda suka gabaceka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane gaba dayansu? sai ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu yi salloli biayr a yini da dare? ya ce: "Eh ya Allah ne.” ya ce Ina maka magiya da Allah shin Allah ne Ya umarceka da mu yi azumin wannan watan a shekara? ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce; Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawan mu? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Eh ya Allah". sai mutumin ya ce; na yi imani da abinda ka zo da shi, kuma ni manzo ne na wadanda ke bayana cikin mutane na, Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi