Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

103 daga cikin katuna 839

Cire tacewa

Mai ruwaya

Nuna duk masu ruwaya (52)
Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alokacin yana kan mimbari, me kake gani a kan sallar dare, sai ya ce: «Biyu-biyu ce», idan ya ji tsoron (ɓullowar) Asuba sai ya sallaci raka'a ɗaya, sai ta yi masa wutirin abin da ya sallata» kuma shi ya kasance yana cewa «Ku sanya ƙarshen sallarku ta zama witiri» domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da shi.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Da a ce mutane suna sanin abinda ke cikin kiran sallah (na lada) da kuma sahu na farko sannan ba za su samu ba sai idan sun yi ƙuri'a a kansa da sun yi ƙuri'a, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin gaggawa (zuwa sallah a farkon lokaci) da sun yi gasar zuwa gare shi, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin sallar dare (Issha) da Asuba da sun zo musu koda da jan ciki ne».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai: Akan goshi sai ya yi nuni da hannunsa akan hancinsa, da hannaye, da gwiwoyi, da gefunan diga-digai, kuma kada ka tufke tufafi ko gashi".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Lallai wasu mutane sun zo wa Sahlu ɗan Sa'ad Al-sa'idiy alhali sun yi musu a sha'anin minbarin (Manzon Allah) katakwayensa na mene ne, sai suka tambaye shi game da hakan, sai ya ce: Na rantse da Allah ni na san na mene ne su, haƙiƙa na gan shi a farkon ranar da aka ajiye shi, da kuma farkon ranar da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fara zama a kansa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika zuwa ga wance - wata mace daga Mutanen Madina -Sahlu ya ambace ta -; "Ki umarci yaronki kafinta ya haɗa min katakwaa da zan zauna a kansu idan zanyiwa mutane magana". Sai ta umarce shi sai ya yisu daga bishiyoyin daji, sannan ya zo da su, sai ta aika zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya yi umarni aka ajiyesu a nan, sannan na ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a kansu ya yi kabbara alhali yana kansu, sannan ya yi ruku'u alahali yana kansu, sannan ya sauko da baya, sai ya yi sujjada a asalin minbarin sannan ya dawo, yayin da ya gama sai ya fuskanci mutane sai ya ce: "ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"A kwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu, akwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu" sannan ana uku ya ce: "Ga wanda ya so".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Sallar jam'i ta fi sallar ɗayanku shi kaɗai, da yanki ashirin da biyar, kuma mala'ikun dare da mala'ikun rana suna taruwa a sallar Asuba" Sannan Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Lallai karatun alfijir (sallar Asuba) ya kasance abin halartowar (mala'iku) ne} [al-Isra'i: 78].
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koya mana Istikhara a cikin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Alƙur'ani, yana cewa: «Idan ɗayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi (sallah) raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce: Ya Allah ni ina neman zaɓinKa da saninKa, kuma ina neman ikonKa da ikonKa, ina roƙonKa daga falalarKa mai girma, domin cewa Kai Kana da iko ni ba ni da iko, kuma Kana sani ni kuma bani da sani, kaine Masanin abinda ke ɓoye, ya Allah idan Kasan cewa wannan al'amarin alheri ne a cikin Addinina, da rayuwata da ƙarshen al'amarina» ko cewa ya yi: "Magaggaucin al'amarina da kuma majirkincinsa, to ka kaddara mini shi kuma ka sawwaka mini shi sannan Ka yi albarka gareni a cikinsa, idan kuma Kasan cewa wannan al'amarin sharri ne gareni a cikin Addinina da rayuwata da karshemn al'amarina" ko cewa ya yi: "A cikin magaggaucin al'amarina da majirkincinsa, to ka kawar da shi daga gareni ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alheri a duk inda yake, sannan Ka yarda da ni" Ya ce: "Sai ya ambaci buƙatarsa».
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
Dan Zubair ya kasance yana cewa a bayan kowacce Sallah idan ya yi sallama: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki na Sa ne, kuma godiya ta Sa ce, kuma Shi mai iko ne a kan komai. Ba dabara ba ƙarfi sai da Allah, babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi, Shi Ya ke da ni’ima da falala, Shi ke da kyawawan yabo, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsarkake addini gare shi, ko da kafirai sun ƙi. Ya kuma ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗinsu bayan kowacce sallah.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi