عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Rukunoni
Rukunoni (21)
Darajar hadisi
An ruwaito a
Nuna sauran majiyoyi
Mai ruwaya
Nuna duk masu ruwaya (49)
Lallai wasu mutane sun zo wa Sahlu ɗan Sa'ad Al-sa'idiy alhali sun yi musu a sha'anin minbarin (Manzon Allah) katakwayensa na mene ne, sai suka tambaye shi game da hakan, sai ya ce: Na rantse da Allah ni na san na mene ne su, haƙiƙa na gan shi a farkon ranar da aka ajiye shi, da kuma farkon ranar da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fara zama a kansa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika zuwa ga wance - wata mace daga Mutanen Madina -Sahlu ya ambace ta -; "Ki umarci yaronki kafinta ya haɗa min katakwaa da zan zauna a kansu idan zanyiwa mutane magana". Sai ta umarce shi sai ya yisu daga bishiyoyin daji, sannan ya zo da su, sai ta aika zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya yi umarni aka ajiyesu a nan, sannan na ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a kansu ya yi kabbara alhali yana kansu, sannan ya yi ruku'u alahali yana kansu, sannan ya sauko da baya, sai ya yi sujjada a asalin minbarin sannan ya dawo, yayin da ya gama sai ya fuskanci mutane sai ya ce: "ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"A kwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu, akwai sallah tsakanin dukkan kiran sallah biyu" sannan ana uku ya ce: "Ga wanda ya so".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Sallar jam'i ta fi sallar ɗayanku shi kaɗai, da yanki ashirin da biyar, kuma mala'ikun dare da mala'ikun rana suna taruwa a sallar Asuba" Sannan Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Lallai karatun alfijir (sallar Asuba) ya kasance abin halartowar (mala'iku) ne} [al-Isra'i: 78].
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koya mana Istikhara a cikin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Alƙur'ani, yana cewa:
«Idan ɗayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi (sallah) raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce:
Ya Allah ni ina neman zaɓinKa da saninKa, kuma ina neman ikonKa da ikonKa, ina roƙonKa daga falalarKa mai girma, domin cewa Kai Kana da iko ni ba ni da iko, kuma Kana sani ni kuma bani da sani, kaine Masanin abinda ke ɓoye, ya Allah idan Kasan cewa wannan al'amarin alheri ne a cikin Addinina, da rayuwata da ƙarshen al'amarina» ko cewa ya yi: "Magaggaucin al'amarina da kuma majirkincinsa, to ka kaddara mini shi kuma ka sawwaka mini shi sannan Ka yi albarka gareni a cikinsa, idan kuma Kasan cewa wannan al'amarin sharri ne gareni a cikin Addinina da rayuwata da karshemn al'amarina" ko cewa ya yi: "A cikin magaggaucin al'amarina da majirkincinsa, to ka kawar da shi daga gareni ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alheri a duk inda yake, sannan Ka yarda da ni" Ya ce: "Sai ya ambaci buƙatarsa».
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
Dan Zubair ya kasance yana cewa a bayan kowacce Sallah idan ya yi sallama: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki na Sa ne, kuma godiya ta Sa ce, kuma Shi mai iko ne a kan komai. Ba dabara ba ƙarfi sai da Allah, babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi, Shi Ya ke da ni’ima da falala, Shi ke da kyawawan yabo, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsarkake addini gare shi, ko da kafirai sun ƙi. Ya kuma ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗinsu bayan kowacce sallah.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai ɗayanku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: Ina shaida wa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce; Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sannan ya ce; Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa sallah, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa tsira, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sai ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah daga zuciyarsa zai shiga aljanna".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Wanda ya yi sammako zuwa masallaci ko ya maraita, Allah zai tanadar masa wani masauki a cikin aljanna duk lokacin da ya yi sammako ko ya maraita".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi