Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

74 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Cewa Ummu Salama ta gayawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta ga wata coci a kasar Habasha, ana kiranta Mariya, sai ta fadi duk abubuwan da ta gani a can na Hotuna, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa, kuma su yi masa wadannan hotunan, wadannan su ne ashararen mutane a wajen Allah".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayin wata sallah ba bayan saukar: {Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} [al-Nasr: 1] ta sauka gare shi sai ya ce a cikinta (sallar): "Tsarki ya tabbatar maKa Ubangijinmu da godiyarKa ya Allah Ka gafarta mini'.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na rasa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wani dare a shinfiɗa sai na lalube shi sai hannuna ya faɗa akan cikin diga-digansa alhali shi yana cikin masallaci alhali su suna a kafe, alhali shi yana cewa: "Ya Allah ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da kuma rangwaminKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gareKa ba zan iya ƙididdige yabo gareKa ba kamar yadda Ka yabi kanKa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana buɗe sallah da kabbara, da kuma karatu, da (faɗar) Alhamdu lillahi rabbil aalamina (Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai), ya kasance idan ya yi ruku`u ba ya ɗago kansa, ba kuma ya miƙar da shi saidai tsaka-tsaki, ya kasance idan ya ɗago kansa daga ruku`i ba ya yin sujjada, har sai ya daidaita a tsaye, ya kuma kasance idan ya ɗago kansa daga sujjada, ba ya kuma sujjada har sai ya daidaita a zaune, ya kasance yana yin tahiya a bayan kowace raka`a biyu, ya kasance yana shimfiɗa ƙafar sa ta hagu ya kuma kafe ƙafar sa ta dama, ya kasance yana yin hani gameda irin zaman shaiɗan. sannan yana yin hani mutum ya shimfiɗa hannayen sa guda biyu irin shimfiɗawar namun daji, ya kasance yana rufe sallar da yin sallama.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Idan an tsaida sallah to babu wata sallah sai ta farilla kawai».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla: "babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne godiya tasa ce, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, ba mai bayar da abin da Ka hana, mai wadata wadatarsa bata amfanar da shi (komai) a wajenKa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa", kuma cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an zo masa da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa daga maɓungura ƙasa, sai ya ji wari daga gareta, sai ya yi tambaya sai aka ba shi labarin abinda ke cikinta na maɓungura ƙasa, sai ya ce ku kusantar da ita ga wani daga sahabbaina wanda ke tare da shi, lokacin da ya ganta sai ya ƙyamaci cinta, ya ce: "Ka ci domin cewa ni ina ganawa da wanda ba ka ganawa (da shi)".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi