Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

41 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Mushirikai suka ce mana: Lallai cewa ni ina ganin abokin nan naku yana koya muku (abubuwa) har yana koya muku biyan buƙata, sai ya ce: Eh, Lallai cewa shi ya hana ɗayanmu ya yi tsarki da (hannun) damansa, ko ya fuskanci alƙibla, kuma ya yi hani daga (tsarki) da toroson dabbobi ko ƙasusuwa kuma ya ce: «‌Kada ɗayanku ya yi tsarki da ƙasa da duwatsu uku».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Ku rage gashin baki, ku cika gemu".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na halarci Amr dan Abu Hassan ya tambayi Abdullahi dan Zaid game da alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce a kawo masa kwarya ta ruwa, sai ya yi musu alwala irin alwalar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya sanya hannunsa akwaryar, sai ya wanke hannayensa sau uku, sannan ya shigar da hannunsa a cikin kwaryar, sai ya kuskure baki ya shaka ruwa ya face, kanfata uku, sannan ya shigar da hannunsa sai ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya wanke hannayensa sau biyu zuwa gwiwar hannu, sannan ya shigar da hannunsa sai ya shafi kansa, sai ya yi gaba da su ya yi baya sau daya, sannan ya wanke kafafuwansa zuwa idan sawu.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikeni wata bukata, sai na samu janaba ban samu ruwa ba, sai na tumurmusa a bigire kamar yadda dabba take tumurmusa , sannan na zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na ambata masa hakan sai ya ce: "Kadai ya isheka ka aikata kamar haka da hannayenka" sannan ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ni ina yin jinin cuta bana tsarkaka, shin zan bar sallah ne? sai ya ce: "A'a, Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya kai zuwa jujin wasu mutane, sai ya yi fitsari a tsaye, sai na yi nesa, sai ya ce: "ka kusanto" sai na kusanto har na tsaya daura da maƙyangymansa sai ya yi alwala sai ya yi shafa akan kuffinsa biyu.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Babu wani musulmin da zai yi alwala ya kyautata alwalarsa, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, yana mai fuskantarsu da zuciyarsa da fuskarsa, sai aljanna ta wajaba gareshi" Ya ce: Sai na ce: Ya mamakin kyan wannan, sai ga wani mai magana a gabana yana cewa: Wacce ke gabanta ta fi kyau, sai na duba sai ga Umar ya ce: Lallai ni na ganka ka zo ɗazu, ya ce: "Babu wani daga cikinku da zai yi alwala sai ya kai matuƙa - ko sai ya cika - alwalar sannan ya ce: Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne sai an buɗe masa kofofin aljanna takwas zai shiga ta wacce yake so".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi