Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

8 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Lallai cewa tawaida da layu da tiwala (tsafin juyar da tunani musamman tsakanin ma'aurata) shirka ne".
Ingantacce ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad.
Cewa shi ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah; Shin bana nuna maka wata mace daga cikin 'yan aljanna ba? na ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar da ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Ni ina farfaɗiya kuma inayin tsirara, to ka roƙamin Allah, ya ce: «‌Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki» ta ce: Zan yi haƙuri, ta ce : To cewa inayin tsirara to ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara, sai ya roƙa mata.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Wasu mutane daga Ukl ko Urainah suka zo (wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -), sai suka ƙyamaci zama a Madina sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce su suje gurin raƙuman (zakka), kuma su sha fitsarinsu da nononsu, sai suka tafi, lokacin da suka samu lafiya sai suka kashe mai kiwon (dabbobin) Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suka kora dabbobin, sai labari ya zo a farkon yini, sai ya aika aka bi bayansu, lokacin da rana ta ɗaga sai aka zo da su, sai ya yi umarni a yanke hannayensu da ƙafafuwansu, kuma aka tsire idanuwansu, aka jefasu a cikin zafin rana, suna neman a shayar da su ruwa amma ba'a shayar da su ba. Abu Ƙilabah ya ce: Waɗannan sun yi sata sun yi kisa, sun kafirta bayan sun yi imani, sun yaƙi Allah da ManzonSa.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Cewa (Mala’ika) Jibril ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Muhammad baka da lafiya ne? sai ya ce: «‌Eh» ya ce: «‌Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan abinda zai cutar da kai, daga sharrin kowane rai ko maitar mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Ka sanya hannunka akan wurin da kake jin raɗaɗin daga jikinka, ka ce: Da sunan Allah sau uku, kuma ka ce sau bakwai “Ina nema tsarin Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji kuma nake tsoro".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wajan mara lafiya yana yi masa addu'a zai ce : «Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu wata waraka sai warakarKa, warakar da bata barin wata masassara».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wanda ya duba mara lafiya (wanda) ajalinsa bai yi ba, sai ya ce a wurinsa sau bakwai: Ina roƙon Allah Mai girma Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya, sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar".
Ingantacce ne Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad
"Lallai zan bai wa wani mutum wannan tutar Allah Zai yi buɗi ta hannunsa, yana son Allah da manzaonSa kuma Allah da manzonSa suna son shi". Ya ce: Sai mutane suka kwana suna tattaunawa a daran waye a cikinsu za'a ba shi ita, lokacin da mutane suka wayi gari sai suka yi jijjifi ga manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - kowanne su yana ƙaunar a ba shi ita, sai ya ce: "Ina Aliyu ɗan Abi Dalib?" sai aka ce : Shi ya manzon Allah yana ciwon idanu, ya ce: "Ku aike masa", sai aka zo da shi sai manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tofi a cikin (idanuwa) ya yi masa addu'a, sai ya warke kai kace babu wani ciwo a tare da shi, sai ya ba shi tuta, sai (Sayyidina) Aliyu ya ce: Ya manzon Allah, shin zan yake su ne har sai sun zama irinmu? sai ya ce: "Ka zarce a hankali har sai ka sauka a farfajiyarsu, sannan ka kira su zuwa ga musulunci, ka ba su labari da abinda yake wajaba akansu na hakkin Allah a cikinsa, na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da kai shi ne mafi alheri daga jajayen ni'imomi (rakuma)".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi