عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Rukunoni
Darajar hadisi
An ruwaito a
Mai ruwaya
Cewa shi ya zo wurin Hajarul Aswad (Baƙin dutse) sai ya sumbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi cewa shi ya fada a sha'anin mutane Madina: "Ba mai sonsu sai mumini, kuma babu mai kinsu sai munafiki, wanda ya so su Allah zai so shi, wanda ya ki su Allah Zai ki shi".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Lallai Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya nemiSabitu ɗan Ƙais (domin bai ganshi ba) sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan samo maka labarinsa, sai ya zo masa sai ya same shi a zaune a gidansa ya sunkuyar da kansa, sai ya ce: Meke damunka? sai ya ce: Sharri, ya kasance yana ɗaga sautinsa sama da sautin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, to, haƙiƙa aikinsa ya ɓaci, kuma shi yana daga 'yan wuta.
Sai mutumin ya zo sai ya ba shi labarin cewa kaza da kaza, sai ya dawo a karo na ƙarshe da babban albishir, sai ya ce: "Ka tafi zuwa gareshi ka ce masa: Lallai kai ba ka cikin 'yan wuta, sai dai kana daga cikin 'yan aljanna".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Mafi alherinku zamanina, sannan waɗanda suke biye musu, sannan waɗanda suke biye musu» Imran ya ce: Ban sani ba shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agatre shi - bayan nan ya ambaci ƙarni biyu ne ko uku, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai a bayanku za'a samu wasu mutane zasu dinga ha'iinci ba'a amince musu ba, sunayin shaida ba tare da an nemi shaidarsu ba, suna bakance ba sa cikawa, kuma ƙiba zata bayyana a cikinsu».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi