Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

29 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
A cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi} [al-haj: 25] ya ce: "Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi".
Ingantacce ne Ahmad da Hakim ne suka ruwaito shi
Lokacin da mutuwa ta zo wa Abu Dalib, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo masa sai ya samu Abu jahal da Abdullahi Dan Abu Umayyah Dan Mugira a wurrinsa, sai ya ce: "Ya kai baffana, ka ce : Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kalma ce wacce zan kafa maka hujja da ita awurin Allah", sai Abu jahal da Abdullahi dan Abu Umayyah suka ce : Kana kin tafarkin Abdul Muddalib, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai gushe ba yana bijiro masa da ita, suma suna maimaita masa waccan maganar, har Abu Dalib ya ce karshen abinda ya fada musu: Akan tafarkin Abdul Muddalib ya ki fadar: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wallahi zan nemamaka gafara muddin ba'a hanani ba". Sai Allah yaYa saukar da: {Bai kasance ga Annabi ba da wadanda suka yi imani da su nema wa mushrikai gafara ba} [Al-Taubah: 113], kuma Alllah Ya saukar asha'anin Abu Dalib, sai Ya cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: {Lallai kai ba zaka shiryar da wanda kake so ba sai dai Allah Yana shiryar da wanda Ya so} [Al-Kasas: 56].
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«‌Ku karanta Alƙur’ani domin zai zo ranar alƙiyama yana mai ceton ma'abotansa, Ku karanta surori biyu Baƙara da al-Imran, domin cewa su za su zo a ranar alƙiyama kamar giza-gizai ko kamar wata tawagar tsuntsaye sun yi sahu, suna kare ma'abocinsu, ku karanta Surat al-Baƙara don haddace ta albarka ne, kuma barinta asara ne, kuma matsafa ba zasu iya ta ba».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Na kasanace a wurin minbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai wani mutum ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai kawai in shayar da mai yin aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa, sai Umar ya yi musu tsawa, kuma ya ce: Kada ku ɗaga muryarku a wajen mimbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali ranar Juma'a ce, sai dai idan na sallaci Juma'a zan shiga in tambaye shi a cikin abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Shin yanzu kwa mayar da shayar da mai aikin Hajj da kuma raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira}[al-Taubah: 19] karanta ayar har zuwa ƙarshenta.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Lokacin da waɗannan ayoyin suka sauka: {Lallai Mu mun yi maka buɗi buɗi mabayyani dan Allah Ya gafarta maka} har zuwa faɗinSa: {Rabo mai girma} [al-Fath: 1-5] lokacin dawowarsa daga Hudaibiyya, alhali su baƙin ciki da ɓacin rai yana cakuɗe da su, alhali haƙiƙa annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya soke hadayarsa a Hudaibiyya, sai ya ce: "Haƙiƙa an saukar mini da wata aya ita ce mafi soyuwa gareni daga duniya da abinda ke cikinta baki ɗaya".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba.
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Lallai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka, sai ya ce: "Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su, sabo da haka mutane sun kasu biyu: Mai biyayya ga Allah kuma mai tsoronSa mai girma a wajen Allah, da kuma fajiri taɓaɓɓe wulaƙantacce a wajen Allah, mutane 'ya'yan (Annabi) Adam ne, kuma Allah Ya halicci Annabi Adam daga turɓaya, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ya ku mutane lallai Mun halicce ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wurin Allah shi ne mafificinku a tsoron Allah, lallai Allah Masani ne kuma mai ba da labari [Al-Hujrat: 13].
Ingantacce ne Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shi