Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

3 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
A cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi} [al-haj: 25] ya ce: "Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi".
Ingantacce ne Ahmad da Hakim ne suka ruwaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba.
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune kafirai} [al-Ma'idah: 44], da {Waɗannan sune azzalimai} [al-Ma'ida: 45] da kuma {Waɗannan sune fasiƙai} [al-Ma'ida: 47]. ya ce: Ibnu Abbas ya ce: Allah Ya saukar da ita ne saboda ƙungiyoyi biyu daga cikin Yahudawa, ɗayarsu ta kasance ta rinjayi ɗayar a lokacin Jahiliyya, har suka yadda suka yi sulhu akan cewa dukkanin wadda aka kashe to wacce ta yi rinjayen (babbar kabilar) ta kashe shi daga cikin ƙasƙantacciya (wacce aka yi nasara a kanta) to diyyarsa ita ce Wusƙi hamsin, kuma dukkanin wadda aka kashe wadda ƙasƙantacciyar ta kashe shi daga mai rinjayen to diyyarsa ita ce Wusƙi ɗari, sun kasance akan haka har Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina, dukkanin ƙungiyoyi biyun suka miƙa wuya ga zuwan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wannan lokacin bai yi rinjaye galaba, kuma bai haɗasu a kansa ba, shi yana cikin sulhu, sai ƙasƙantacciyar ta kashe wani daga cikin mai rinjayan, sai mai rinjayen ta aika zuwa gurin ƙasƙantacciyar: Ku aiko mana da Wusƙi ɗari, sai ƙasƙantacciyar ta ce: Shin wannan ya kasance ne a cikin ƙabilu biyu kawai Addininsu ɗaya, nasabarsu ɗaya, garinsu ɗaya, diyyar sashinsu rabin diyyar sashi ce? Mu ɗin nan mun baku wannan ne kawai dan zalincinku a garemu, da rinjayen da kuka yi mana, amma tunda (Annabi) Muhammad ya zo to baza mu baku hakan ba, sai yaƙi ya kusa ya kunnu a tsakaninsu, sannan suka yarda su sanya Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tsakaninsu, sannan wacce ta yi galabar ta ambata sai ta ce: Wallahi (Annabi) Muhammad ba zai baku daga cikinku ninkin abin da suke basu daga garesu ba, kuma haƙiƙa sun yi gaskiya, ba su bamu wannan ba sai dan zalincin da muke yi, da kuma rinjayarsu da muka yi, dan haka ku yi dassi zuwa ga (Annabi) Muhammad wanda zai binciko muku ra'ayinsa: Idan ya baku abin da kuke so to sai ku sanya shi mai hukunci, idan kuma bai baku ba sai ku kiyaye shi, ba zaku sanya shi mai hukunci ba, sai suka yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dassin wasu mutane daga cikin munafukai dan su basu labarin ra'ayin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai Allah Yaba ManzonSa labarin gabaɗayan al'amarinsu da kuma abin da suka yi nufi, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Yakai Manzo kada waɗanda suka yi gaggawa cikin kafirci daga waɗanda suka ce mun yi imani su baƙanta maka rai}[al-Ma'ida: 41] har zuwa faɗinSa: {Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune fasiƙai}[al-Ma'idah: 47] sannan ya ce: Wallahi ta sauka ne a cikin sha'aninsu, kuma sune Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yake nufi.
Hasan ne Ahmad ne ya rawaito shi