Skip to content

Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana i'itikafin goman ƙarshe na Ramadan, har Ya koma ga Allah , sannan matansa suka yi i'itikafi a bayansa

Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -:

Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana i'itikafin goman ƙarshe na Ramadan, har Ya koma ga Allah , sannan matansa suka yi i'itikafi a bayansa.

أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَعْتَكِفُ العَشْرَ الأَوَاخِرَ مِنْ رَمَضَانَ، حَتَّى تَوَفَّاهُ اللَّهُ، ثُمَّ اعْتَكَفَ أَزْوَاجُهُ مِنْ بَعْدِهِ.

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya lazimci i'itikafi a goman ƙarshe na Ramadan, dan neman Lailatul Qadr, kuma ya zarce akan hakan har zuwa lokacin da Allah Ya ɗauki ransa, haƙiƙa matansa - Allah Ya yarda da su - sun lazimci i'itikafi a bayansa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Halaccin i'itikafi a cikin masallatai, har ga mata akan wasu iyakoki na shari'a, da kuma sharaɗin aminta daga fitina.

I'itikafi yana ƙarfafa a cikin goman ƙarshe na Ramadan saboda lazimtar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

I'itikafi Sunna ne mai zarcewa ba'a shafe shi ba, dan matansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun yi i'itikafi a bayansa.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (3/ 47) (2026).

Sahih Muslim (2/ 831) (1172).

Kari (4)

تيسير العلام.

لعبد الله البسام (ص351).

تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام.

لابن عثيمين (3/ 474).