Lallai cewa idan ɗayanku ya mutu za’a bijiro masa da mazauninsa safiya da maraice
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Lallai cewa idan ɗayanku ya mutu za’a bijiro masa da mazauninsa safiya da maraice, idan ya kasance daga cikin 'yan aljanna ne to yana daga cikin 'yan aljanna, idan ya kasance daga cikin 'yan wuta to yana daga cikin 'yan wuta, sai a ce: Wannan mazauninka ne har sai Allah Ya tasheka ranar alƙiyama".
«إِنَّ أَحَدَكُمْ إِذَا مَاتَ عُرِضَ عَلَيْهِ مَقْعَدُهُ بِالْغَدَاةِ وَالعَشِيِّ، إِنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ الجَنَّةِ فَمِنْ أَهْلِ الجَنَّةِ، وَإِنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ النَّارِ فَمِنْ أَهْلِ النَّارِ، فَيُقَالُ: هَذَا مَقْعَدُكَ حَتَّى يَبْعَثَكَ اللَّهُ يَوْمَ القِيَامَةِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa bawa idan ya mutu za'a bijiro masa da masaukinsa da gurinsa na musamman a cikin aljanna ko wuta, a farkon yini da ƙarshensa; wurinsa a aljanna idan ya kasance daga cikin 'yan aljanna, da kuma wurinsa a wuta idan ya kasance daga cikin 'yan wuta ne, kuma za’a ce masa: Wadannan wuraran ne wadanda za'a tasheka zuwa gare su ranar alƙiyama; a cikin hakan akwai ni'imtarwa ga mumini, da kuma azabtarwa ga kafiri.
Azabar ƙabari da ni'imarsa gaskiya ne.
Ibnu Hajar ya ce: Lallai wannan bijirowar ga mumini mai tsoron Allah da kuma kafiri zahiri ne, amma mumini wanda ya cakuɗa ayyukansa sai a ɗauka akan cewa za'a bijiro masa da mazauninsa na aljannar da zai tafi zuwa gareta.
Sahih Al-Bukhari (2/ 99-100) (1379).
Sahih Muslim (4/ 2199) (2866).
Kari (6)
عمدة القاري شرح صحيح البخاري.
لبدرالدين العيني (8/ 209).
التنوير شرح الجامع الصغير.
لمحمد الصنعاني (2/ 209).
الإفصاح عن معاني الصحاح.
ليحيى بن هبيرة (4/ 131).
An ambata a cikin littattafai
2 LittattafaiKari (2)
- أحكام الجنائز(إِنَّ أَحَدَكُمْ إِذَا مَاتَ عُرِضَ عَلَيْهِ مَقْعَدُهُ بِالْغَدَاةِ وَالْعَشِيِّ إِنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ فَمِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ، وَإِنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ النَّارِ فَمِنْ أَهْلِ النَّارِ، فَيُقَالُ: هَذَا مَقْعَدُكَ حَتَّى يَبْ
- مجموعة زاد الحديث(2)1«إن أحدكم إذا مات عُرِضَ عليه مقعدُه بالغداةِ والعَشِي، إن كان من أهل الجنةِ فمن أهل الجنةِ، وإن كان من أهل النار فمن أهل النار، يقال: هذا مقعدُك، حتى يبعثَك الله يومَ القيامةِ».