مقدمة وغلاف المنتقى من موسوعة الأحاديث النبوية
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Allah Ya yi tsira Ya yi aminci ga Annabinmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki ɗaya, da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:
Lallai daga mafi girman abinda yake wajaba musulmi ya kula da shi; a karantawa da lura da jujjuya ma'anoni, da ilimi da aiki - bayan littafin Allah - (shi ne kula da) sunnar manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, (Manzon Allah) tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: "Na barmuku yaku mutane, abinda idan kuka yi riƙo da shi, ba zaku taɓa ɓata ba har abada: Littafin Allah, da sunnar Annabinsa" Imam Malik ne ya ruwaito shi , Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Abinda manzo ya zo muku (da shi) to ku riƙe shi abinda kuma ya haneku to ku hanu} [al-Hashr: 7]. Saboda haka ne Gidauniyar hidimar abinda Musulunci ya ƙunsa da Harsuna da kuma Gidauniyar Da'awa da wayar da kan Jaliyoyi (waɗanda ba 'yan ƙasa ba mazauna ƙasar Saudiyya) a Rabwah akan tanadar : BAKANDAMIYA HADISAN ANNABI (SWA). Da fassara su da akan adadi masu yawa na Harsuna.
Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sawwaƙa zaɓin wani kaso na wannan BAKANDAMIYAR wadda musulmi yake buƙatarta a cikin al'amarin Addininsa da duniyarsa, tare da takaitaccan bayani akansu, da bayyanar da ma'anoninsu da abinda suke nunarwa, da wasu daga fa'idodinsu, da fitar da su a cikin wannan littafin da aka ambace shi da: "TATACCIYAR BAKANDAMIYAR HADISAN ANNABI". (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Aiki yana ci gaba sosai akan fassarasu zuwa dukkanin rayayyun Harsuna a duniya dan anfani ya game da abinda suka ƙunsa na isar da sunnar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga mutane a harsunan su.
Muna roƙon Allah Ya karɓi wannan aikin, ya kuma sanya shi aikine mai albarka, abin tsarkakewa ga zatinsa mai girma, kuma Ya sakawa dukkan wanda ya taimaka akan shirya shi da fassara shi da kuma yaɗa shi.
Allah Ya yi daɗin tsira ya yi aminci ga Annabinmu Muhammad.
Taƙaitaccen bayani
Hadisan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, su ne tushe na biyu daga tushen shara'antawa, (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: {Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa (3) (Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa} [al-Najm: 3-4].
Wannan Tataccan daga Bakandamiyar hadisai, ya ƙunshi wani kaso na hadisai da suka tattaro (ma'anoni), daga abinda musulmi yake buƙatar shi a cikin al'amarin Addininsa da duniyarsa tare da bayani taƙaitacce a gare su, da bayyanar da ma'anoninsu da abinda suke nunawa, da wasu daga fa'idodinsu waɗanda aka fassara a wani adadi daga rayayyun harsunan duniya, dan anfani ya game da abinda suka ƙunsa, da isar da sunnar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga mutane a harsunan su.